Yaki da ta'addanci a Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa wasu mayakan 'yan ta'dda sun kutsa hukumar Kanam da ke jihar Filato tare da sace Hakimin yankin da wasu mata guda biyu.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dauki wasu manyan alkawura biyar ga jihar Katsina domin yaƙar ’yan ta’adda, ciki har da samar da jirage marasa matuƙa.
A labarin nan, za a ji yadda fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ja kunnen jami'an tsaro a kan zaman sulhun Katsinawa da 'yan ta'adda.
An bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya umarci sufeton 'yan sandan Najeriya da a dauki matakan hana 'yan bindiga samun makamai a Najeriya da suke kai hari.
A labarin nan, za a ji yadda yan ta'adda su ka zauna da hukumomi da su ka hada da jami'an gwamnati a jihar Katsina domin kawo karshen kisan bayin Allah.
Rundunar ’yan sanda a Zamfara ta cafke fitaccen jagoran ’yan bindiga Muhammadu Kan Kani, yayin da a Imo da Rivers aka kama mambobin IPOB/ESN guda biyar.
Sojojin Operation FANSAN YANMA sun kashe ’yan ta’adda biyu a Kaduna, sun kwato makamai da babura bakwai a Katsina, yayin da rahoto ya fayyace dalilan rushewar sulhu.
Dalibai bakwai sun jikkata a Ukum, Benue bayan wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya tashi a makarantarsu. ‘Yan sanda da gwamnati sun dauki matakai kan lamarin.
‘Yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne sun kashe hakimi a Sokoto, yayin da suka tilasta mutane tserewa daga gidajensu saboda hare-haren da suke kaiwa ba kakkautawa.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari