Ana Shirin Tafiya Hajji, DSS Sun Cafke Karin 'Yan Ta'adda da aka Jima Ana Nema
- Jami'an DSS su kama wasu da ake zargi da ta’addanci a Sakkwato da Abuja yayin tantance maniyyatan Hajjin bana a filayen jirgin sama
- An kama Yahaya Zango a filin jirgin saman Abuja, wanda ake zargi da ta'addanci da kuma hannu a garkuwa da mutane a Abuja da Kogi
- Hukumomi na kara kaimi wajen tantance maniyyata Hajji, bayan an gano an tura wasu da ake zargi da ta’addanci zuwa Saudiyya a 2024
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama wasu manyan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a Sakkwato da Abuja, yayin da ake tantance maniyyatan aikin Hajji.
Wata majiya ta shaida cewa an kama Aliyu Sani Galadi, wanda aka fi sani da Mai Boxer, an kama shi ne a ranar Litinin da ta gabata a filin jirgin Sultan Abubakar dake Sakkwato.

Asali: Twitter
AIT Live ta wawallafa cewa Aliyu Sani Galadi, wato Mai Boxer, dan asalin karamar hukumar Shinkafi ne a jihar Zamfara, kuma jami'an DSS sun dade suna bin sawunsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSS sun kama yan ta'adda a Abuja
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa an kama Ayuba Zakariyya da ake zargi da ta'addanci a kusa da kauyen Sheda, dake karamar hukumar Kwali, a Abuja.
Rahoton ya ci gaba da cewa an kama Yahaya Yakubu ne a wajen sansanin Hajji na Abuja da ke Gwagwalada, yayin da aka kama Aminu Auwal a unguwar Paikon Kore, cikin karamar hukumar Gwagwalada.

Asali: Twitter
Kamen wadannan mutane na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan DSS ta jagoranci wasu jami’an tsaro wajen cafke Yahaya Zango, wanda ake zargi da garkuwa da mutane a filin jirgin saman Abuja a ranar Lahadi da ta gabata.
An kama wanda ake zargi da ta'addanci a Kogi
Rahoton ya ce an kama Zango ne yayin tantance wasu maniyyata da ke shirin tashin zuwa kasa mai tsarki ta filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, ana zarginsa da ta'addanci a Kogi.
Zango yana zaune ne a unguwar Paikon Kore da ke cikin karamar hukumar Gwagwalada, kuma dukkan su biyar sun dade suna kan jerin sunayen da DSS ke sanya ido a kansu.
A shekarar 2024 ne aka bayyana damuwa bayan rahotanni sun nuna cewa akwai ‘yan ta’adda 14 da aka tura aikin Hajji zuwa Saudiyya.
An cafke mutum uku daga cikinsu bayan dawowarsu gida, yayin da aka saki daya daga cikinsu a wani yanayi da har yanzu ba a bayyana gaskiyarsa ba.
A halin yanzu, hukumomin tsaro na kara kaimi wajen tantancewa da tattara bayanan sirri domin hana maimaituwar irin wannan lamari a bana.
An kama iyalan rikakken dan ta'adda
A baya, kun ji cewa rahotanni na cewa hukumomin tsaron Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargi da alaka da shahararren jagoran ‘yan bindiga a Najeriya, Ado Aliero.
Jami'an tsaron Najeriya dai na neman Ado Aliero ruwa a jallo bisa laifuffuka da dama da suka hada da ta’addanci da garkuwa da mutane da hana zaman lafiya a yankin Zamfara da kewaye.
Rahotanni sun tabbatar da cewa matan da ake zargi sun hada da mahaifiyar Ado Aliero da kuma daya daga cikin matansa, yayin da suka ziyarce ziyarce a kasa mai tsarki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng