Lokaci Ya Yi: Tsohon Shugaban PDP Ya Gamu da Ajalinsa da Ya Koma Gida Neman Abinci

Lokaci Ya Yi: Tsohon Shugaban PDP Ya Gamu da Ajalinsa da Ya Koma Gida Neman Abinci

  • Ƴan bindiga sun hallaka tsohon shugaban PDP a matakin mazaɓa, James Akase tare da wasu mutum uku a jihar Benuwai
  • Maharan sun kashe mutane da dama a hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban a kananan hukumomin Gwer ta Yamma da Guma
  • Har yanzu rundunar ƴan sandan jihar Benuwai ba ta ce komai ba game da waɗannan sababbin hare-hare na ƴan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na gunduma, James Akase, tare da wasu mutum uku, sun rasa rayukansu a hare-hare daban-daban da ƴan bindiga suka kai a jihar Benuwai.

Maharan sun kai hare-hare lokuta daban-daban kan mutanen garuruwa biyu a kananan hukumomin Gwer ta Yamma da Guma na jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Jihar Benue.
Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban PDP a jihar Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Shaidu sun bayyana cewa an kashe su ne a ranar Litinin a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a yankunan karkara da ke yankin Guma da Gwer ta Yamma, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma ruwaito cewa wasu mutane sun samu raunuka a hare-haren, waɗanda yanzu haka suna kwance ana kula da su a asibitoci daban-daban a wuraren da hare-haren suka faru.

Yadda aka kashe tsohon shugaban PDP

Bayanai sun nuna cewa tsohon shugaban PDP da aka kashe ya jima da barin gidansa da ke garin Tse-Defam, Mba’akov Vengav, yankin Avihijime a karamar hukumar Gwer ta Yamma.

James Akase ya bar gidansa ne saboda barazanar kai masa hari, sai dai an kashe shi a lokacin da ya koma garinsu domin neman abinci ga iyalansa.

A karamar hukumar Guma kuwa, mutum uku sun rasa rayukansu a ranar Litinin yayin wani hari da ƴan ta'adda suka kai kauyen Tse Ikpe Ago da ke kan titin Yogbo-Gyungu Aze da kauyen Tse Kologa.

Mahara sun kashe wasu mutum 3 a Guma

Mazauna garin sun ce an kashe mutum ɗaya mai suna, Bartholomew Ikornya a Tse Ikpe Ago, yayin da a Kologa kuwa, Gabriel Korlaga da wani mai suna Kunde suka rasa rayukansu.

Shugaban karamar hukumar Gwer ta Yamma, Victor Ormin, ya tabbatar da kisan tsohon shugaban PDP, James Akase a wata tattauna ta wayar salula.

Yan sanda.
Yan sanda sun yi shiru kan sababbin hare-haren da aka kai a jihar Benue Hoto: Nigiria Police Force
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa maharan sun sace wani mutum a yankin, amma an sake shi da dare bayan iyalansa sun biya kudin fansa, rahoton Daily Post.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Benue, CSP Catherine Anene, bata dauki wayar salula ba yayin da aka kira ta domin samun karin bayani.

An kashe sama da mutum 20 a Benuwai

A wani rahoton, kun ji cewa aƙalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu tsakanin ranar Juma’a da Asabar sakamakon sababbin hare-hare a wasu ƙauyukan Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe waɗannan bayin Allah ne a lokacin da suke hanyar zuwa gonakinsu.

Hare-haren ƴan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne na ƙaruwa a jihar Benuwai, wanda ya sa aka fara kiraye-kirayen ayyana dokar ta ɓaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262