'A cikin Makonni Muka Murkushe Boko Haram,' Atiku Ya Fadi Dabarun Gwamnatin Obasanjo

'A cikin Makonni Muka Murkushe Boko Haram,' Atiku Ya Fadi Dabarun Gwamnatin Obasanjo

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya murkushe Boko Haram cikin makonni kadan tun farkon bayyana kungiyar a shekarar 2002
  • Tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa Obasanjo ya yi tsayin daka wajen korar kungiyar Boko Haram
  • Atiku ya dora alhakin sake bullowar Boko Haram da matsalar rashin tsaro gaba ɗaya kan rashin jajircewar shugabannin da suka biyo bayan Obasanjo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya murkushe Boko Haram cikin gaggawa tun farkon bayyanarsu a 2022.

Atiku ya fadi hakan ne a ranar Laraba yayin da wasu jiga-jigan siyasa daga Kogi ta Gabas suka kai masa ziyara, karkashin jagorancin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Simon Achuba.

Obasanjo
Atiku ya fadi yadda gwamnatinsu ta Obasanjo ta kawo karshen Boko Haram Hoto: @Rasheethe
Asali: Twitter

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa shafinsa na Facebook, Atiku ya alakanta nasarar da aka samu a wancan lokacin wajen fatattakar 'yan ta’addan da irin karfin gwiwar da gwamnatin Obasanjo ta nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya bayyana farkon bayyanar Boko Haram

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a cewar Atiku, kungiyar Boko Haram ta fara bayyana ne a Jihar Yobe a shekarar 2002, wanda hakan ya sa Obasanjo ya nemi shawararsa domin daukar mataki cikin gaggawa.

Atiku ya ce:

“Ka tuna lokacin da Boko Haram ta fara a Yobe? Muna cikin ofis. Shugaban kasa ya kira ni, ya ce: 'Me za mu yi game da wannan?' Sai na ce: 'Mu kira manyan hafsoshin tsaro, mu basu wa’adin lokaci. Idan ba za su iya magance matsalar ba, to su ajiye mukamansu. Za mu nemo wasu da za su iya yin aiki.’”

Yadda Obasanjo ya murkushe Boko Haram

Atiku ya bayyana cewa Obasanjo ya dauki matakin gaggawa inda ya kira shugabannin tsaro tare da basu umarni na musamman, kuma a cikin makonni kadan an shawo kan lamarin.

Atiku
Atiku ya dora alhakin rashin tsaro a kan shugabannin Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

“Ya kira manyan hafsoshin tsaro, ina wajen a lokacin, ya ba su umarni kai-tsaye, kuma a cikin makonni kadan suka murkushe 'yan Boko Haram a Yobe. Tun daga lokacin ba ta sake fitowa ba har sai da muka bar mulki.”

Atiku ya dora alhakin sake dawowar Boko Haram da yawaitar rashin tsaro a Najeriya kan rashin jajircewar shugabannin da suka biyo bayan gwamnatin Obasanjo.

Ya ce:

“Zan ce rashin karfin gwiwar shugabannin ne matsalar. Idan ana kashe ‘yan kasa, ya za ka zauna ka ci abinci? Ana kashe jama’arka amma kai ba ka damu ba; wannan shi ne mafi girman rashin kishin kasa da wani shugaba zai iya nunawa.”

Ya kara da cewa:

“Saboda haka, ina dora laifin dukkanin wannan matsalar tsaro da ke faruwa a fadin kasa kan shugabancin da mu ke da shi.”

Atiku ya caccaki shugaba Bola Tinubu

A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar EFCC ke ci gaba da keta dokar kasa ta hanyar cafke mutane.

A cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar, ya bayyana cewa takaici ne ganin yadda EFCC ke amfani da damar kama mutane musamman masu sukar gwamnati domin tsoratar da su.

Atiku ya yi magana ne bayan EFCC ta cafke tsohon dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure, sannan aka kai shi Abuja ba tare da sanarwa ko bayani ga iyalansa ko lauyoyinsa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.