Atiku Abubakar Ya Jero Waɗanda Yake Zargi da 'Kawo Matsalar Tsaro' a Najerirya
- Atiku Abubakar ya zargi shugabannin da suka biyo bayan Olusegun Obasanjo da sakaci, wanda ya jawo matsalar tsaro
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce a lokacin da suke mulki, ba su ɗauki barazanar Boko Haram da wasa ba
- Atiku ya ce shugabannin da ke kan mulki ba su damu da rayuwar al'umma ba, yana mai cewa bai kamata su iya cin abinci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da ƴan ta'adda ke ƙara zafafa hare-hare a ƴan kwanakin nan a Najeriya, Atiku Abubakar ya taɓo tushen matsalar tsaron da ta hana jama'a zama lafiya.
Tsohon matainakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sakacin shugabannin da suka zo bayan Olusegun Obasanjo ne ya haifar da matsalar tsaro.

Asali: Twitter
Kamar yadda Channels tv ta tattaro, Atiku ya yi wannan furuci ne da ya karɓi bakuncin wasu manyan siyasa daga yankin Kogi ta Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan Wazirin Adamawa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Su wa Atiku ke zargi da kawo matsalar tsaro?
Atiku ya zargi shugabannin da suka zo bayan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da gazawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da kyale ƙungiyoyin ta’addanci su yaɗu.
Wannan zargi na Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP suka kai wasu munanan hare-hare kan dakarun sojoji a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun kashe sojoji, sannan sun kwashi makamai nadu dimbin yawa daga sansanin dakarun.
Da yake tsokaci kan halin da ake ciki a yankin da ya fito watau Arewa maso Gabas, Atiku ya ce matsalar da ake ciki laifin shugabannin da suka gaji Obasanjo ne.
Atiku Abubakar ya ce::
“Ina dora laifin dukkan matsalolin tsaro da ke faruwa a sassan ƙasa kan shugabannin da suka zo bayan Obasanjo.”
'Dan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023 ya ce Obasanjo ya nuna jajircewa wajen murkushe ƙungiyar Boko Haram tun lokacin da ta fara fito da kanta a jihar Yobe shekaru fiye da 20 da suka wuce.

Asali: Twitter
Atiku Abubakar ya soki shugabannin Najeriya
Atiku ya ci gaba da cewa:
"Abin da ke faruwa ya nuna rashin ƙarfin gwiwa da gazawar shugabanci daga waɗanda ke mulki.
"Ta ya ana kashe mutanenka, har za ka iya cin abinci? Ana kashe ‘yan ƙasarka, kai kuma ko a jikanka, wannan ne mafi girman rashin kula daga kowane irin shugaba."
Boko Haram ta shafe fiye da shekaru 15 tana tayar da hankali a Najeriya, inda ta kashe fiye da mutane 40,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu, tana fafutukar kafa daular Islama a yankin.
Atiku ya sake sukar gwannatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan yadda gwmanatin Bola Tinubu ke karya dokokin kasa ta hanyar kama jama'arta.
A cewarsa, cafke tsohon dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure a Kano aka kai shi Abuja ba tare da bayani ba ya saɓawa takadin doka.
Gudaji Kazaure ya kasance daya daga cikin ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Bola Tinubu kan yadda ake tafiyar da al’amuran kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng