"Ba Za a Samu Zaman Lafiya a Arewa nan da Shekaru 10 ba," Uba Sani Ya Jero Dalilai 3

"Ba Za a Samu Zaman Lafiya a Arewa nan da Shekaru 10 ba," Uba Sani Ya Jero Dalilai 3

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce talauci, matsin tattalin arziki da rashin aikin ne tushen matsalar tsaron da ake fama da ita a Arewa
  • Malam Uba Sani ya ce matukar shugabannin Arewa ba su haɗa hannu wuri ɗaya ba, yankin zai ci gaba da fuskantsar matsaloli
  • Gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a daina amfani da ƙarfin soji kaɗai domin sai an magance rashin aikin yi da talauci kafin a yi nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa talauci da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan dalilan da ke kawo matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Ya ce sai an fuskanci wadannan matsaloli ta hanyar hadin gwiwa da tsari mai kyau, in ba haka ba, yankin zai ci gaba da fuskantar rikice-rikice.

Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani ya ce talauci da rashin aikin ne suka jawo matsalar tsaro a Arewa Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Gwamna Uba Sani ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV a shirin Sunday Politics.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam.Uba Sani ya ce:

“Ni ɗan gwagwarmaya ne, na fafata da gwamnatoci tun lokacin mulkin soja. Na shiga kurkuku saboda neman adalci da daidaito.”

Uba Sani ya jingina matsalar tsaro da talauci

Gwamnan ya ce lokacin da ya hau karagar mulki, ya fara ne da nazarin ma’aunin talauci da ci gaban tattalin arziki a Kaduna da Arewa baki daya, inda ya bayyana cewa:

“A lokacin da na zama gwamna a 2023, sama da kashi 60 zuwa 65 cikin 100 na mutanen Arewa, musamman Arewa maso Yamma ba su da wata dama ta samun kudi.
"Wannan ya sanya matasa da dama suke da saukin daukar makami ko shiga kungiyoyin 'yan bindiga.”

Yadda yara ke gararamba a Arewa

Gwamnan ya kuma bayyana cewa sama da yara 350,000 ne ke ke gararamba a gari ba tare da suna zuwa makaranta ba a lokacin da ya karbi mulki a Kaduna.

"Mun zauna mun yi nazari tare da Mataimakin Shugaban Bankin Duniya da kuma UNICEF. A cikin yara miliyan 18.2 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, Arewa na da fiye da kashi 70%.”
"Wannan rashin tsaro da muke fama da shi, ina tabbatar muku cewa matsin tattalin arziki, talauci da rashin aiki ne suka kawo shi.
“Ba zan ce za mu warware wannan matsala gaba daya cikin shekaru 10 ba. Domin matsalar ta dade tana tasowa. Mun yi shiru, ba mu dauki matakan da ya dace ba.”

- Uba Sani.

Uba Sani.
Uba Sani ya buƙaci shugabannin Arewa su haɗa kai domin magance matsalolin yankin Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Gwamna Uba Sani ya bukaci shugabannin Arewa da su hade kai wuri guda domin fuskantar wannan matsala da gaske.

Ya jaddada cewa akwai buƙatar ganin cewa kowane dan Arewa ya samu dama da ci gaba ta kowace fuska, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Matsalar tsaro a Arewa

Arewacin Najeriya na fama da matsalar tsaro mai tsanani tun tsawon shekaru da dama, lamarin da ya shafi rayuwar miliyoyin mutane tare da jefa yankin cikin matsaloli da cikas na ci gaba.

Yankin na fuskantar matsaloli da dama ciki har da barnar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane don neman kudin fansa, rikice-rikicen kabilanci, da hare-haren ta’addanci daga kungiyoyi kamar Boko Haram da ISWAP.

Wadannan kungiyoyi suna kaiwa kauyuka, makarantu, da wuraren ibada hari, suna kashe mutane da lalata dukiya.

Dalilin da yasa ta'addanci ya yi yawa

Talauci, rashin aikin yi, da rashin ilimi suna kara tabarbarewar lamarin, inda matasa da dama ke shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda saboda rashin wata hanya ta samun rayuwa.

Rashin ci gaban tattalin arziki da karancin ababen more rayuwa suna hana mutane samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya da ilimi, lamarin da ke kara ta’azzara matsalar tsaro.

Haka kuma, rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya kan filaye da albarkatu suna kara jefa yankin cikin tashin hankali.

Kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi na kawo karshen matsalar ya hada da ayyukan soja da tattaunawa, amma matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa na nan daram.

Rashin hadin kai tsakanin shugabannin siyasa da na gargajiya na kawo tsaiko wajen magance matsalar.

Sai an magance manyan tushen matsalar kamar talauci da rashin aikin yi, matsalar tsaro za ta ci gaba da addabar Arewa.

Uba Sani ya yabi Shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya jinjinawa ƙoƙarin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi a Najeriya tun da ya karɓi mulki.

Uba Sani ya ce babu wata gwamnati da ta zuba jari tare da inganta harkar noma kamar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya kara da cewa shugaba Tinubu ya dauki matakan da suka rage ƙarfin talauci musamman a Arewacin Najeriya cikin shekaru biyu da hawansa kan madafun iko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262