'Kashi 80 na Matsalolin Tsaro da Suka Addabi Sakkwato na da Alaka da Miyagun Kwayoyi'

'Kashi 80 na Matsalolin Tsaro da Suka Addabi Sakkwato na da Alaka da Miyagun Kwayoyi'

  • Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ce kusan 80% na matsalolin tsaro a jihar na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi
  • Ahmed Aliyu ya jaddada cewa mutumin da ke cikin hayyacinsa ba zai iya kashe wani ba, yana mai danganta hakan da tasirin ƙwayoyi
  • Ya ce yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba aikin hukumomi kaɗai ba ne, sai an haɗa kai da iyaye, malamai, sarakuna, malaman addini da sauran al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaron da jihar ke fuskanta na da nasaba da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Gwamna Ahmed ya ce wannan annoba na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar makomar matasa da ci gaban al’umma.

Gwamna Ahmed.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu yana magana a wurin kaddamar da wasu ayyukan gwamnatinsa Hoto: Abdulrahman Muhd Dogondaji
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa mai girma gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wani taron lakca da aka shirya domin tunawa da Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta 2026.

Miliyoyin yan Najeriya na shan kwayoyi

A Maris na shekarar 2026, gidauniyar Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 14.3 ne ke amfani da miyagun kwayoyi, inda matasa suka fi yawa a cikin wadanda abin ya shafa.

Gidauniyar ta bayyana lamarin a matsayin wata matsalar gaggawa ta kasa da ke bukatar daukar matakan hadin gwiwa daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Yadda shaye-shaye ke ruguza tsaro

Da yake jawabi ta bakin mataimakinsa, Alhaji Idris Mohammed Gobir, Gwamna Ahmed ya ce mafi yawan laifuffukan tashin hankali da ayyukan ‘yan bindiga a jihar na da alaka da amfani da miyagun kwayoyi.

Ya ce:

“Kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaron da ke addabar jiharmu na da alaka da miyagun kwayoyi. Wadannan mutane suna amfani da kwayoyi masu hadari. Mutum mai hankali ba zai kalli wani mutum ya kashe shi ba.”

A cewarsa, shaye-shayen miyagun kwayoyi na rusa iyalai, hana matasa cimma burinsu, sannan yana taimakawa wajen yawaitar aikata laifuffuka tare da haifar da matsalolin lafiya da zamantakewa.

Gwamna ya bukaci matasa su guji shaye-shaye

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar Sakkwato na son ganin matasa sun zama shugabanni a nan gaba maimakon fadawa tarkon miyagun kwayoyi.

Ya ce:

“Muna son ku zama shugabannin kasa, ministoci, gwamnoni da shugabannin manyan kamfanoni a Najeriya. Amma ba za ku iya cimma hakan ba idan kuka shiga shaye-shayen miyagun kwayoyi ko safararsu.”
Sokoto.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bukaci hadin gwiwar al’umma

Gwamna Ahmed Aliyu ya jaddada cewa yaki da miyagun kwayoyi ba aikin hukumomin kadai ba ne, akwai bukatar hadin kai daga kowane bangare, kamar yadda Punch ta kawo.

Ya ce iyaye, malamai, shugabannin addini da na gargajiya, kungiyoyin fararen hula, ma’aikatan lafiya, shugabannin al’umma da kafafen yada labarai dole su hada hannu wajen magance matsalar.

Gwamnatin Sakkwato ta dauki matakai

A baya, kun ji cewa Gwamnatin jihar Sakkwato ta kwantar da hankulan jama'a kan rade-radin da ake yadawa cewa Bello Turji ya sayo sababbin makamai.

Ta ce hukumomin tsaro suna da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a yankunan da ke fama da matsalar ‘yan bindiga, kuma suna daukar matakan dakile duk wata barazana.

Gwamnatin ta ce ba za ta raina kowace barazana ba, amma tana da yakinin cewa jami’an tsaro suna da kwarewa da shirin fuskantar duk wani kalubale.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262