Boko Haram: Rundunar Soji Ta Magantu kan Bidiyon Yiwa Sojoji Kisan Wulakanci
- Rundunar soji ta karyata bidiyon da ake cewa daga harin Marte ne, wanda ke nuna yadda Boko Haram ta yi wa dakaru kisan gilla
- An zargi ‘yan ta’adda da yada bidiyo domin yaudarar jama’a da kuma rage ƙwarin gwiwar sojoji da suka sadaukar da rayuwarsa ga kasa
- Rundunar ta sha alwashin kama masu yada ƙarya tare da gurfanar da su a kotu domin dakile mugun nufin masu goyon bayan ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rundunar tsaro ta ƙasa ta karyata wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta da ake yadawa da cewa daga harin da 'yan ta’adda suka kai wa sojoji a Marte, jihar Borno, kwanan nan ne.
Rundunar ta bayyana cewa bidiyon ba shi da alaƙa da harin da ya faru a ranar 12 ga Mayu, 2025, inda ta ce abin da ke cikin bidiyon ya faru ne tun a watan Disambar shekarar 2020.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan hulɗa da manema labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya fitar a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram: An binciki bidiyon kisan sojoji
Jaridar PR Nigeria ta ce bincike da aka gudanar kan bidiyon ya bayyana cewa yankin da aka dauki bidiyon, hoton bidiyon da kuma halin da ake ciki lokacin, ba su da wata alaƙa da abin da ya faru kwanan nan a Marte.
Kangye ya zargi masu goyon bayan 'yan ta’adda da miyagun mutane da cewa su ne ke yawan sabunta tsofaffin bidiyo domin yaudarar jama’a da kuma rage ƙwarin gwiwar sojoji.
Ya ce:
"Sojojin AFN da ke Marte sun gamu da harin ‘yan ta’adda a ranar Litinin, 12 ga Mayu, 2025 da 3.00 na safe. Sai dai sojojin sun fatattaki ‘yan ta’addan bayan musayar wuta mai zafi inda da dama daga cikinsu aka kashe su, wasu kuma suka tsere da raunukan harbi."
An soki masu yada bidiyon Boko Haram
Kangye ya bayyana yada tsohon bidiyon a matsayin mugun yunkuri na haifar da tsoro, bata sunan aikin sojoji da kuma ɓata wa jama’a rai game da rundunar tsaro.

Asali: Facebook
Ya ce:
"'Yan ta’addan sun yanke shawarar yada tsohon bidiyo a matsayin farfaganda domin yaudarar masu karamin tunani. Wannan aikin yaɗa ƙarya ba wai kawai mugunta ba ce, har ma da yunkurin wuce gona da iri na karya gwiwar jaruman sojojinmu da kuma rage amincewar ‘yan Najeriya da rundunar soji."
Ya sha alwashin cewa rundunar soji za ta gano wadanda ke da hannu a yaɗa irin wannan ƙarya tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Harin Boko Haram ya girgiza jama'a
A wani labarin, kun ji cewa a ci gaba da farmakin ta’addanci da kungiyar ISWAP ke ka iwa a yankin Arewa maso Gabas, ta kai mumanan hare-hare a kan sansanonin soji a jihohin Borno.
Mayakan ISWAP sun kitsa hare-hare a kan sansanonin soji hudu a Marte, Rann, da Gajiram a kasa da awanni 48 tare da illata jami'an soji da dama, da kashe wadansu daga cikinsu.
A halin yanzu, akwai fargaba a tsakanin al’umma game da yawaitar hare-haren da ake kaiwa cikin dan kankanin lokaci, yayin da rundunar soji ta ce tana bakin kokarinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng