NASFAT Ta Ja Hankalin Musulmai, Ta Nemi Su Taimaka kan Matsalar Tsaron Najeriya

NASFAT Ta Ja Hankalin Musulmai, Ta Nemi Su Taimaka kan Matsalar Tsaron Najeriya

  • Kungiyar NASFAT ta Osogbo a jihar Osun ta bukaci Musulmi su mara wa kokarin yaki da rashin tsaro baya a Najeriya
  • 'Dan takarar gwamnan APC a jihar Osun, Bola Oyebamiji, ya yi alkawarin shugabanci na gaskiya da tsoron Allah idan ya yi nasara
  • NASFAT ta bayyana nasarorin da ta samu a bangaren ilimi, lafiya, tallafa wa mabukata da karfafa tattalin arzikin mambobinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Kungiyar Nasrul-lahi-l-Fatih Society of Nigeria (NASFAT) ta bukaci Musulmi a fadin Najeriya su mara wa kokarin da ake yi na yaki da matsalar rashin tsaro baya.

Shugaban NASFAT reshen Osogbo, Alhaji Tajudeen Adisa Jimo, ne ya bayyana hakan a Osogbo, babban birnin jihar Osun, yayin bikin cika shekaru 25 da kafuwar reshen kungiyar.

NAFSAT.
Mambobin kungiyar NAFSAT a taron cika shekaru 25 da aka gudanar a Osogbo, jihar Osun Hoto: Lateef Adewale
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa a wajen taron da ya samu halartar sarakunan gargajiya, malamai da ‘yan siyasa, Jimo ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a sassan kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sakkwato ta yi magana kan rahoton da ake yadawa game da Bello Turji

Kungiyar NAFSAT ta bada mafita

Jimo ya jaddada cewa shawo kan ta’addanci da sauran manyan laifuffuka ba zai yiwu ba sai da hadin gwiwar jama’a, jami’an tsaro da gwamnatoci a matakai daban-daban.

A nasa bangaren, Sheikh Sulaiman Faruq Onikijipa (Al-Miskeen Bilahi), wanda ya gabatar da lakca a wajen taron, ya yaba wa NASFAT bisa gudunmawar da take bayarwa ga Musulmi da al’umma baki daya.

Ya bayyana bikin cika shekaru 25 a matsayin wata dama ta waiwayar baya domin tantance ci gaba da kuma kara dankon zumunci tsakanin jama’a.

'Dan takarar APC ya dauki alkawari

Ɗan takarar gwamnan jihar Osun na jam’iyyar APC a zaben 15 ga watan Agusta, Bola Oyebamiji, wanda shi ma mamba ne na NASFAT, ya yi alkawarin gudanar da mulki cikin tsoron Allah idan ya samu nasara.

Oyebamiji ya ce zai tabbatar da gaskiya, rikon amana da manufofin da za su amfani al’umma domin bunkasa ci gaban jihar Osun, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ba makamin azabatarwa ba ne"; Atiku ya nuna damuwa kan sharuddan belin El Rufai

Ya ce:

“Ni Musulmi ne mai kishin addini kuma ba zan ba ku kunya ba. Idan muka shiga gwamnati, za ku ga kyawawan dabi’un Musulunci a shugabanci da gudanar da mulki.”
NASFAT.
Dan takarar gwamnan jihar Osun na APC, Bola Oyebamiji tare da Sheikh Sulaiman Farouq a taron kungiyar NASFAT Hoto: Lateef Adewale
Source: Facebook

NASFAT ta lissafo nasarorin da ta samu

Shugaban NAFSAT, Jimo ya ce daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu akwai kafa makarantu masu araha, asibitoci, gudanar da gwaje-gwajen lafiya kyauta da ayyukan tiyata ga mabukata

A cewarsa, kungiyar ta kuma kammala tare da bude makabarta ta Musulmi, sannan tana gudanar da shirin tallafin kudi ga mambobi 400 duk shekara a watan Ramadan.

Sauran ayyukan sun hada da bayar da jari da kayan aiki ga masu sana’o’i, tallafin abinci ga marasa karfi, samar da filaye da gidaje ga mambobi da kuma shirye-shiryen koyar da harshen Larabci da tarukan addini.

Kungiyar JNI ta bukaci a yi addu'a

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ta bukaci Musulmi su yi addu’ar neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma, Sarkin Musulmi ya yi umarni da addu'a saboda 'makiyan Najeriya'

Kungiyar ta bayyana cewa za a yi addu’o’in ne domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen matsalolin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar Najeriya.

JNI ta ce Sarkin musulmi ya bukaci Musulmi su kasance masu tsoron Allah, masu biyayya ga dokoki, masu zaman lafiya da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262