'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Najeriya Ta Sayo Wa Sojoji Manyan Makamai 'Masu Haɗari'
- Najeriya sayo manyan makamai da nufin kawo ƙarshen hare-haren Boko Haram, ISWAP, ƴan bindiga da dukan nau'in ta'addanci
- Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai jihar Borno ranar Alhamis
- Ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shirya tsaf domin dawo da zaman lafiya, ya roki ƴan Najeriya su ba da haɗin kai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Babban hafsan hafsoshin tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa rundunar sojin kasar ta sayo sababbin makamai masu inganci.
Christopher Musa ya ce rundunar ta cefano manyan makamai ne domin yaki da ’yan ta’adda a fadin Najeriya.

Asali: Twitter
Ya faɗi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a wata ziyara da ya kai yankin Arewa maso Gabas ranar Alhamis, The Cable ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Musa ya tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa babu dalilin da za su riƙa fargaba, domin dakarun sojoji za su shawo kan lamarin tsaro da ya dame su.
Najeriya ta sayo wa sojoji ƙarin makamai
Ya bayyana cewa matsin lambar da aka yi wa ’yan ta’adda a yankin Sahel ne ke kara tilasta musu kai hare-hare a Najeriya, musamman a yankin Tafkin Chadi.
"Mun sayo sababbin makamai masu haɗari da inganci, za a fara amfani da su tare da sababbin dabarun da za mu ɓullo da su domin kawo ƙarshen ta'addanci.
"Bai kamata hare-haren da miyagu ke kawowa lokaci bayan lokaci ya firgita mutane ba, domin dakarun soji da sauran jami'an tsaro na kan lamarin, kuma ba abin da ya sha ƙarfinsu."
“Abin da ke faruwa yanzu sakamako ne na matsin lambar da ’yan ta’adda ke fuskanta a Sahel, wanda ya sa suke yawaita hare-hare a Najeriya, musamman a iyakokin da ke kusa da Tafkin Chadi. Amma muna aiki tuƙuru domin magance hakan.”
- Janar Christopher Musa.
Musa ya kara da cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Asali: UGC
Sojoji na bukatar haɗin kan ƴan Najeriya
Ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su mara wa sojoji baya, yana mai jaddada cewa tsaro aiki ne na kowa da kowa.
"Tsaro ba na mutum guda ba ne. Ina kira ga kowane ɗan ƙasa ya taimaka a yaki da Boko Haram, ISWAP, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wani nau’in laifi domin zaman lafiya da ci gaban Najeriya,” in ji shi.
Ya ce da ya kai ziyara Rasha kwanan nan, "Najeriya ta nanata matsayarta na dogaro da kai amma mun tattauna da masu ruwa da tsaki da suka shirya haɗa kai da mu a fagen yaƙi."
Janar Musa ya gana da manyan jami'ai da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai a barikin Maimalari, sannan ya ziyarci sansanin Giwa a Maiduguri.
Sojoji sun zargi 'dan sa-kai da cin amana
A wani rahoton, kun ji cewa sojoji na zargin wani jami'in CJTF da haɗa kai da ƴan ta'addan Boko Haram wajen kai masu hare-hare a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa bayan hare-haren, sojoji sun fara guduwa daga sansanoninsu domin tsira da rayuwarsu.
Majiyoyin soji, da suka yi magana a ranar Talata bisa sharadin sakaya sunansu, sun ce wasu daga cikin sojojin da harin ya rutsa da su sun kama hanya sun koma cikin iyalansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng