Borno: Boko Haram na Warware Aikin Jami'an Tsaro, Ta Kashe Manoma 90 cikin Watanni
- Mayakan Boko Haram da ISWAP sun kai munanan hare-hare a yankin tafkin Chadi, suka kashe manoma da masunta akalla 90
- A ranar 15 ga Mayu, 2025, mayakan ISWAP sun kai hari a wata gona, kuma sun hallaka kashe akalla manoma 50 da jikkata wasu
- Amnesty International ta bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa a kan Boko Haram domin kare rayuwar fararen hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Akalla manoma da masunta 90 ne suka rasa rayukansu a hare-hare da wasu ƙungiyoyin 'yan bindiga suka kai a yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno cikin watanni biyar.
An zargi mayakan Boko Haram da na ISWAP da kai haren-haren, inda suka kashe mutane da dama, wasu kuma suka jikkata ko suka yi garkuwa da su.

Asali: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa hare-haren sun faru ne tsakanin watan Janairu da Mayu 2025, kuma sun bar mummunan tasiri a kan al’ummar yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram na ta'adi a jihar Borno
A sabon hari da aka kai ranar 15 ga Mayu, 2025, mayakan ISWAP sun afka wa wata gonar wake da ke Malam Karanti a ƙaramar hukumar Kukawa, suka kashe akalla manoma 50.
Majiyoyi sun ce wasu mayakan Boko Haram ne suka kai wa manoman hari a yankin da ke ƙarƙashin ikon ISWAP, wanda ke kusan kilomita 9 daga garin Baga.
Wani daga cikin mazauna yankin ya ce manoman da masuntan sun dade suna samun kariya daga wani kwamandan ISWAP kafin wannan hari ya faru.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Suna da takardun izini daga kwamandan da ke kula da Malam Karanti har zuwa Dawashi. Sun dade suna samun kariya daga gare shi, mai suna Amir Akilu, bayan sun biya haraji.”
Amnesty ta zaburar da gwamnati kan Boko Haram
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan yadda mayakan Boko Haram ke ci gaba da kashe jama’a ba tare da tsoron hukuma ba.
Shugaban kungiyar a Najeriya, Sanusi Isa, ya shaidawa Legit cewa:
“Yanzu an shiga wani hali inda mutane ke cikin bala’i, kuma waɗannan 'yan bindiga suna cin karensu babu babbaka. Wuraren da aka taɓa kwace daga hannunsu yanzu suna ƙara dawowa hannunsu.”
“An yi tufka, ana yin warwara. Wannan bala’i ne da ke jefa rayuwar farar hula cikin masifa.”
Sanusi Isa ya bukaci gwamnatin tarayya da ta maida hankali sosai wajen yaki da Boko Haram kafin matsalar ta sake lalacewa gaba ɗaya a Borno da sauran yankunan arewa maso gabas.
Gwamna Zulum ya sa dokoki a Borno
A baya, mun wallafa cewa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rattaba hannu kan sababbin dokoki guda biyu da suka shafi kare muhalli da inganta rayuwar al’umma a jihar.
Zulum ya sanya hannu kan dokar da ta haramta sare itatuwa ba tare da izini ba, da kuma wata doka da ta wajabta gudanar da aikin tsaftar muhalli na wata-wata a duka fadin jihar.
Zulum ya bayyana cewa matakin ya zama wajibi ganin yadda ake sare itatuwa ba tare da bin ka'ida ba, wanda ke haddasa tabarbarewar muhalli da barazana ga rayuwar al’umma a nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng