Abun Bakin Ciki
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa an harbe wani matashi da bindiga a lokacin bikin naɗin sarauta a Gwoza, jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Jami’an shige da fice biyu sun jikkata bayan wani mutum da ake kira Fasto Darlington ya harbe su bisa kuskuren zargin su 'yan fashi ne da suka zo sata.
Yayin da Arewacin Najeriya ke fuskantar manyan matsaloli, Gwamnoni da sarakunan gargajiya daga jihohin Arewa 19 sun hallara a Kaduna domin tattaunawa.
Bayan yada zarge-zarge kan mataimakin gwamnan Edo, Dennis Idahosa, ya musanta jita-jitar cewa yana da alaka da kungiyoyin asiri, yana mai cewa sharri ne kawai.
Ɗan majalisa a jihar Lagos kuma tsohon ɗan fim, Desmond Elliot ya bayyana yadda ya kusa konewa a ofishinsa a Surulere lokacin zanga-zangar EndSARS a 2020.
Gobara ta lalata gidan amarya da wasu gidaje shida a Zamfara. An ce motocin kashe gobara sun samu matsala, lamarin da ya jawo wutar ta babbake dakin amaryar.
Rahoton da muke samu sun tabbatar da cewa rundunar 'yan sanda ta kama sabon sarkin Ijare, Oba Adekolajo Aladeseyi, da wasu mutane hudu bisa zargin nada kansu.
Majiyoyi sun ce wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani jami’in ‘yan sanda da wani mutum a kauyen Ikyac-Gev da ke Makurdi a jihar Benue.
Kwamishinar jin dadin mata ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ta bayyana yadda wata mata ta zo ofishinta tana neman taimako kan yadda ɗanta ke yi wa mata ciki.
Abun Bakin Ciki
Samu kari