Kwana Ya Ƙare: Shugaban Ƙasa 'Mafi Talauci a Duniya' Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohon shugaban kasar Uruguay wanda a zamaninsa ake kiransa da 'shugaba mafi talauci a duniya', José Mujica ya riga mu gidan gaskiya
- Shugaban Uruguay, Yamandú Orsi ya tabbatar da mutuwar José Mujica wanda aka fi sani da Pepe, yana da shekara 89 da haihuwa a duniya
- An rahoto cewa a lokacin mulkinsa, Pepe ba ya zama a gidan gwamnatin da aka tanada kuma yana hawa wata tsohuwar mota samfurin 1987
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Uruguay - Tsohon shugaban kasar Uruguay, José Mujica, wanda aka fi sani da “Pepe” kuma wanda aka san shi a matsayin “shugaban kasa mafi talauci a duniya” ya riga mu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa ana kiran Pepe a matsayin shugaban ƙasa mafi talauci a duniya ne saboda yadda yake tafiyar da rayuwarsa cikin sauƙi kuma irin ta talakawa.

Asali: Twitter
Shugaban Uruguay na yanzu, Yamandú Orsi, ne ya sanar da rasuwarsa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya, inda ya rubuta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na gode da komai da ka bayar da kuma kauna mai zurfi da ka nuna ga al’ummarka.”
Babu cikakken bayani kan musabbabin mutuwarsa, amma an bayyana cewa yana fama da cutar kansa ta makogwaro. Ya mutu yana da shekara 89 a duniya.
Yadda Pepe ya shugabanci kasar Uruguay
Pepe ya shugabanci Uruguay daga 2010 zuwa 2015 kuma ya shahara da saukin rayuwarsa, ya ƙi da rayuwa ta almubazzaranci da kuma sauye-sauyen da ya jagoranta.
Daga cikin matakan kawo sauyi da ya ɗauka wanda ake tunawa har da halasta amfani da tabar wiwi domin jin dadi, inda Uruguay ta zama ta farko a duniya da ta aiwatar da hakan a hukumance.
Gwagwarmayar José Mujica kafin samun mulki
Kafin zaman shugaban kasa, an kama Pepe sau hudu saboda ayyukansa a kungiyar gwagwarmaya ta MLN-T.
A wani lokaci a 1970, an harbe shi sau shida kuma ya kusa mutuwa amma Allah ya sa da sauran kwanansa a gaba.
Haka nan kuma ya tsere daga kurkuku sau biyu, ciki har da wani fitinannen fashin magarƙama da ya hada da wasu fursunoni 105, daya daga cikin mafi girma a tarihin Uruguay.
Me yasa ake kiransa da shugaban ƙasa mafi talauci?
A lokacin mulkinsa, ya ki komawa gidan gwamnati da aka tanadar wa shugaban kasar Uruguay.
Maimakon haka, ya ci gaba da zama da matarsa, Lucía Topolansky, a wani karamin gida a wajen birnin Montevideo, ba tare da masu aikin gida ko tsauraran matakan tsaro ba.

Asali: Twitter
Ana ganinsa sau da dama yana tuka tsohuwar motarsa, 'Volkswagen Beetle' samfurin 1987. Har ila yau, yana raba mafi yawan albashinsa ga mabukata.
Sai dai duk da haka, Pepe ya musanta kiran da ake masa na “shugaban kasa mafi talauci”. A wata hira da aka yi da shi a 2012, ya ce:
“Ba ni ba ne talaka. Talaka shi ne wanda kullum yana bukatar ƙari, domin yana cikin tseren da ba ya karewa.”
Mace mafi tsufa a duniya ta mutu a Brazil
A wani labarin, kun ji cewa matar da ke riƙe da kambun mace mafi tsufa a duniya, Inah Canabarro Lucas ta mutu tana da shekaru 116 da haihuwa a duniya.
Lucas ta mutu ne a garin Porto Alegre da ke ƙasar Brazil kamar yadda rahotanni daga makusantanta suka tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa an haifi Lucas a ranar 8 ga Yuni, 1908, kuma ta zama mafi tsufa a duniya ne a watan Janairu, 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng