‘Ka Shirya’: Gargadin da Davido Ya Yi ga Gwamnan APC bayan Nasarar Kawunsa a Osun
- Fitaccen mawakin Afrobeats, Davido, ya tura sako ga Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, bayan nasarar kawunsa Ademola Adeleke
- Okpebholo ya yi wa Adeleke ba'a kan yadda yake rawa, yana tambayar ko mutanen Osun sun gaji da ganin gwamnan yana rawa
- Bayan Adeleke ya yi nasara, Davido ya wallafa saƙo a Instagram yana cewa Okpebholo ya shirya, domin zai mayar masa da martani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Shahararren mawakin Afrobeats, Davido, ya yi farin ciki bayan sanar da nasarar Gwamna Ademola Adeleke.
Davido ya sake yi wa Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, gargadi bayan da Gwamna Ademola Adeleke ya samu nasara a zaɓen gwamnan Osun.

Source: UGC
Davido ya yi gargadin ne a Instagram inda ya bukaci gwamnan da ya shirya, a yana mai nuna cewa zai mayar masa da martani kan kalaman da ya yi lokacin yakin neman zaɓe.
Rikicin ya samo asali ne daga wani bidiyon yakin neman zaɓe, inda Okpebholo ya yi wa Adeleke, wanda kuma kawun mawaki Davido ne, ba'a.
A lokacin yakin neman zaɓen dan takarar jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji, wanda aka fi sani da Ambo, Okpebholo ya yi magana kan salon rawa na Adeleke.
Abin da Okpebholo ya fada kan Adeleke
A cikin bidiyon, Okpebholo ya yi wa al'ummar Osun tambaya ko sun gaji da ganin gwamnan nasu yana rawa a lokuta daban-daban.
Ya ce:
"Kafin Adeleke ya sanya hannu kan takarda, sai ya yi rawa, yana tambayar ko al'ummar Osun ba su gaji da hakan ba.
"Adeleke ya shafe shekaru hudu yana rawa, har ma kafin ya ci karin kumallo ko ya sha shayi, sai ya fara rawa."
Okpebholo ya kuma danganta wannan dabi'ar ta Adeleke da zargin rashin halartar wasu tarukan gwamnoni da ake gudanarwa a Abuja.
Bugu da kari, ya yi suka kan yanayin hanyoyin Osun, yana mai cewa har tayoyin motarsa sun rika "rawa da girgiza" yayin da yake tafiya a jihar.

Source: Original
Gargadin Davido ga Okpebholo
Bayan Adeleke ya samu nasara a zaɓen gwamnan Osun, Davido ya wallafa saƙo kai tsaye ga Gwamnan Edo a shafinsa na Instagram.
Davido ya yi wa Okpebholo alama a cikin saƙon, inda ya rubuta:
"Okpebholo ka shirya dan uwana, farko, bari na yi bacci tukuna, gobe da ni da kai ne."
Saƙon ya nuna cewa mawakin, wanda ya kasance yana bibiyar kalaman da ake yi yayin yakin neman zaɓen, yana shirin mayar da martani.
Davido ya magantu kan nasarar kawunsa
An ji cewa shahararren mawakin Afrobeats na Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi murnar nasarar kawunsa Ademola Adeleke a zaben gwamnan Osun.
Davido ya bayyana farin cikinsa jim kadan bayan INEC ta ayyana Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben.
Gwamnan ya samu kuri’u 511,067 inda ya doke dan takarar APC, Munirudeen Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815.
Asali: Legit.ng

