Zaben Osun: Gwamna Adeleke Ya ba Takwaransa na APC Tazara Mai Nisa

Zaben Osun: Gwamna Adeleke Ya ba Takwaransa na APC Tazara Mai Nisa

  • Adeleke ya samu kuri’u 268,957, yayin da dan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu 204,809 bayan tattara sakamakon wasu kananan hukumomi
  • Accord Party ta lashe kananan hukumomi masu rinjaye yayin da APC ta samu nasara a biyar daga cikin wadanda aka bayyana
  • Har yanzu ba a bayyana wanda ya lashe zaben ba, domin sakamakon da aka samu ya shafi wasu ne ne kawai daga cikin kananan hukumomi 30 na Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Osogbo, jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya samu gagarumar tazara kan abokin hamayyarsa na APC, Bola Oyebamiji.

Gwamna Adeleke ya samu nasarar ne bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 14 a zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.

Adeleke Ya Samu Kuri’u 268,957

Bayanan da aka tattara daga cibiyoyin tattara sakamakon INEC sun nuna cewa Adeleke, dan takarar Accord Party, ya samu kuri’u 268,957, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Gwamna Adeleke ya fadi yadda zai kifar da APC

Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC ya samu kuri’u 204,809, wanda ya bar tazarar kuri’u 64,148 tsakanin manyan ‘yan takarar biyu, The Nation ta kawo labarin.

Adeleke ya lashe kananan hukumomi 9

A cikin kananan hukumomi 14 da aka bayyana sakamakonsu, Adeleke ya lashe tara, yayin da APC ta samu nasara a biyar.

A Ede North, Adeleke ya samu kuri’u 35,427, yayin da APC ta samu 10,283. A Osogbo, ya samu 36,480 kan 30,474 na APC. A Ede South, Adeleke ya samu 26,188, yayin da Oyebamiji ya samu 6,219.

Haka kuma, Gwamna Ademola Adeleke ya lashe Iwo da kuri’u 27,085, yayin da APC ta samu 19,660.

APC ta yi nasara a wasu Kananan Hukumomi

APC ta samu nasara a Irepodun, inda ta samu kuri’u 15,713 kan 14,502 na Adeleke. A Obokun, APC ta samu 16,120, yayin da Adeleke ya samu 12,023.

Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Osun ta kuma lashe Ola-Oluwa, Atakunmosa East da Ife South.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Kananan hukumomi 8 da ka iya tasiri wurin samar da wanda zai ci zaɓen

Har yanzu ba a san wanda ya lashe zabe ba

Sakamakon da aka bayyana ya shafi kananan hukumomi 14 ne kawai cikin 30 na Jihar Osun da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya.

Saboda haka, ba za a iya tabbatar da wanda ya lashe zaben ba a yanzu, domin ana ci gaba da tattara sakamakon sauran kananan hukumomi kafin INEC ta bayyana wanda ya samu nasara a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng