Yaro Mai Shekaru 18 Ya Ɗirkawa Ƴan Mata 10 Ciki a Wata 5 Kacal
- Ana zargin cewa wani matashi dan shekara 18 da ke koyon sana’a a Anambra ya yiwa ‘yan mata 10 ciki a wata biyar kacal
- Kwamishinar jin dadin mata ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ta ce mahaifiyar yaron ta zo ofishinta tana neman agaji kan lamarin
- Obinabo ta ce yaron yana yaudarar ‘yan matan ne da alkawarin soyayya da aure, kuma ta ce ta na neman shawarwarin jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Wani yaro mai shekaru 18 da ke koyon sana’a ya ba al'umma mamaki kan abin da ya aikata.
Ana zargin matashin da yake koyon sana'a ya dirkawa wasu yan mata 10 ciki a wata biyar kacal a jihar Anambra.

Asali: Facebook
Yadda matashi ya dirkawa mata 10 ciki
Rahoton Punch ya ce daga cikin wadanda suka dauki cikin har da ‘yar maigidansa da wata yarinyar shagonsu a kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun bayyana cewa hakan ya faru bayan an tura yaron ya koyi sana’a a hannun wani maigidansa.
Amma cikin wata uku ya dirkawa mata ciki wanda ya haɗa da 'yar maigidan da kuma yarinyar kasuwa.
Wannan lamari ne na abin takaici ya sa aka kore shi daga koyon sana’ar da yake yi ba tare da bata lokaci ba.
Kwamishinar jin dadin mata da walwalar al’umma ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ita ce ta bayyana hakan kai tsaye a kafar sada zumunta a yau Laraba.
Yaro ya cigaba da yi wa mata ciki a kauye
Obinabo ta ce lamarin ya kara tsananta bayan yaron ya koma kauyensu da zama gaba daya.
Ta ce:
“Ina bukatar shawara daga jama’a saboda wannan ya fi karfi na.
“Wannan yaro an tura shi koyon sana’a yana da shekaru 18, cikin wata uku ya yiwa ‘yar maigidansa da wata yarinya ciki., an kore shi, cikin wata biyu, ya kara yiwa ‘yan mata takwas ciki a kauye.”

Asali: UGC
An nemi taimako game da halin matashin
Obinabo ta kara da cewa mahaifiyar yaron ta kai karar wannan lamari ofishinta domin neman hanyar shawo kan matsalar.
“Na tambaye shi irin sihirin da yake amfani da shi wajen jan hankalin ‘yan mata zuwa kwanciya da shi, amma ya ce kullum yana ce musu yana sonsu kuma zai aure su idan ya samu dukiya.
“Wannan matsala ta fi karfina saboda shekarun yaron da kuma yawan ‘yan matan da ya yiwa ciki; shi yasa nake bukatar taimako don warwareta.”
Obinabo ba ta bayyana sunan yaron ba, ko na mahaifiyarsa, ko sunan kauyensu ba, amma ta bukaci jama’a su ba da shawara kan abin da za a yi.
Cin zarafin yara a Najeriya
A Najeriya, matsalolin da suka shafi cin zarafin mata da yara, musamman a ƙauyuka da al’ummomi marasa tsari, sun yi kamari matuƙa.
Irin wannan lamari da ya faru a jihar Anambra na bayyana yadda rashin kulawa da tarbiyya, da rashin tsari a cikin al’umma ke haifar da barazana ga lafiyar mata da yarinya.
A ƙauyuka da dama, an fi fama da irin waɗannan matsaloli saboda rashin ilimi, talauci, da kuma rashin tsauraran dokoki da za su kare mutuncin 'yan mata.
Ana yawan samun fyade, yin ciki ba tare da aure ba, da kuma tilasta aure a ƙuruciya, wanda ke jefa yara mata cikin mawuyacin hali.
Cin zarafin mata da fyade (GBV) ya zama ruwan dare a irin waɗannan wurare, kuma galibi ba a kai ga hukunta masu laifi saboda karancin tsaro da rashin yarda da hukumomi.
Lamuran da suka shafi cin zarafi da wulakanci ga mata kamar wanda ya faru a Anambra na ƙara bayyana bukatar tsaurara doka da wayar da kan jama’a.
Gwamnati da al’umma suna da rawar da za su taka wajen dakile irin waɗannan abubuwa da kare rayuwar mata da yara.
Gwamna Soludo ya haramta wa'azi
Kun ji cewa Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya haramta wa’azi a kasuwanni, yana mai cewa hakan na haddasa hayaniya da gurbatar iska.
A cikin wani bidiyo da ya karade intanet, Soludo ya ce duk malamin addini da aka kama yana wa’azi a kasuwa zai biya tarar N500,000.
Shugabannin addini sun caccaki matakin da Soludo ya dauka, suna masu cewa hakan cin zarafin ‘yancin addini ne kuma hari ne kan Kiristoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng