Mataimakin Gwamna na da Alaƙa da Kungiyoyin Asiri? An Samu Bayanai

Mataimakin Gwamna na da Alaƙa da Kungiyoyin Asiri? An Samu Bayanai

  • Mataimakin gwamnan Edo, Dennis Idahosa, ya musanta jita-jitar cewa yana da alaka da kungiyoyin asiri, yana mai cewa sharri ne kawai
  • Idahosa ya ce Emmanuel Agbogun ne ya yada bidiyon da ke zarginsa da wasu manyan ’yan Edo da shiga kungiyoyin asiri ba tare da hujja ba
  • Ya ce ba zai lamunci bata suna ba, yana mai cewa zai dauki matakin doka, tare da kira ga jama'a su goyi bayan yaki da kungiyoyin asiri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin City, Edo - An yi ta yada jita-jita cewa mataimakin gwamnan Edo yana da alaka da kungiyoyin asiri.

Sai dai mataimakin gwamnan, Dennis Idahosa, ya yi karin haske game da neman bata masa suna da ake ƙoƙarin yi.

Mataimakin gwamna ya musanta alaka da kungiyar asiri
Mataimakin gwamnan Edo ya ƙaryata alaka da kungiyar asiri. Hoto: Hon. Dennis Idahosa.
Asali: Facebook

Kungiyar asiri: Mataimakin gwamna ya wanke kansa

Idahosa ya musanta zargin da ake yi masa ne a yau Juma'a 9 ga watan Mayun 2025 a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idahosa ya ce Emmanuel Agbogun ne ya saka bidiyo yana zargin sa da wasu 'yan Edo, amma hakan na kokarin karkatar da yaki da asiri ne.

Ya ce bai taba shiga kungiyar asiri ba, yana mai cewa zai dauki matakin doka, ya kuma bukaci jama'a su goyi bayan yaki da asiri.

Ya ce:

"Na samu labarin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta inda Emmanuel Agbogun ya zarge ni da zama dan kungiyar asiri.
"A cikin wannan bidiyon, Agbogun ya ambaci sunana da na wasu fitattun 'yan Edo yana zarginmu da shiga kungiyoyi asiri.
"Na bayyana karara cewa wadannan zarge-zargen ba su da tushe, sharri ne, kuma wani makirci ne da nufin bata min suna."
Mataimakin gwamna ya magana kan alaƙa da kungiyar asiri
Mataimakin Gwamnan Edo, Dennis Idahosa ya musanta alaƙa da kungiyar asiri. Hoto: Hon. Dennis Idahosa.
Asali: Twitter

Matakin da mataimakin gwamna zai ɗauka kan kazafi

Idahosa ya jaddada cewa zargin ba gaskiya ba ne kuma kokari ne na hana gwamnatin jihar ci gaba da yaki da kungiyar asiri.

Ya ce:

"Zarge-zargen na neman karkatar da hankalin gwamnati daga yakin da take da kungiyar asiri da kuma kokarin dawo da zaman lafiya."

Idahosa ya bayyana bidiyon a matsayin hari kai tsaye a kan halayyarsa, inda ya sha alwashin daukar matakin doka.

"Zan sake maimaita cewa wannan bidiyo kazafi ne, hari ne kai tsaye a kan halayyata, kuma ba zan lamunta ba.
"Zan dauki duk matakan doka domin ganin cewa an hukunta wanda ya wallafa wannan sharri da bata suna."

- Cewar Idahosa

Ya sake jaddada cewa gwamnatin jihar na ci gaba da yaki da kungiyoyin asiri, kuma ba zai taba shiga irin wannan ba.

An zargi Obi da shiga kungiyar asiri

A baya, kun ji cewa wani lamari ya tayar da kura bayan zargin ‘dan takaran LP, Peter Obi na da alaka da kungiyar Pyrates Confraternity.

Sai dai hadiminsa, Valentine Obienyem ya yi gaggawar karyata wannan zargi, ya ce Obi bai da wani hadi da tafiyar kungiyar asiri.

Obienyem ya kawo karshen zarge-zargen da aka yi wa Obi da Namadi Sambo game da wannan sharri da aka yi musu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.