Malami, Mahaddaci Kuma Kwararre a Karatun Kur’ani Ya Bar Duniya a Gombe

Malami, Mahaddaci Kuma Kwararre a Karatun Kur’ani Ya Bar Duniya a Gombe

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana jimami bayan rasuwar malamin Musulunci, yana cewa sun yi rashin mutum na musamman kuma mai daraja daga Gombe
  • Pantami ya bayyana marigayin a matsayin mahaddacin Alƙur’ani, wanda ya yi karatu a Jami’ar Madina, sannan ya kasance masani kan tarihin magabata
  • Ya kuma tuna kyakkyawar mu’amalarsu da ta shafe shekaru 32, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa Aliyu Ladan, Ya shigar da shi Aljannatul Firdaus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana jimaminsa bayan rasuwar malami a Gombe.

An tabbatar da mutuwar Malam Aliyu Ladan wanda aka bayyana a matsayin mutumin kirki kuma mai riko da addinin Musulunci.

Malamin Musulunci ya rasu a Gombe
Farfesa Isa Pantami da marigayi Malam Aliyu Ladan. Hoto: @ProfIsaPantami.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da Farfesa Isa Ali Pantami ya yi a shafinsa na X inda ya bayyana matashin a matsayin mahaddacin Kur'ani.

Kara karanta wannan

'Ba su yi mana ta'aziyya ba': Hadimim marigayi ɗan majalisar tarayya ya soki ADC

Pantami ya yi jimamin rasuwar malami a Gombe

Pantami ya ce ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Malam Aliyu wanda ya ke yi masa lakabi da suna Babana saboda irin gudunmawar da ya ba addini.

Ya ce:

"Har yanzu ina cikin jimami tun bayan da na ji labarin rasuwar ɗan’uwanmu, Malam Aliyu Ladan. Ina kiransa da “Babana” cikin kauna, saboda suna ɗaya suke da mahaifina.
Malam Aliyu Ladan mutum ne mai daraja daga Gombe, ya yi karatu a Jami’ar Madina, kuma masani ne kan labarai masu ban sha’awa na magabatanmu salihai.
Ya kasance mahaddacin Alƙur’ani Mai Girma, mai karatu da murya mai kayatarwa da jan hankali, sannan mutum ne da kullum murmushi ke bayyana a fuskarsa. Hakika, mun yi rashin wani mutum na musamman, wanda ba kasafai ake samun irinsa ba."
An yi rashin malamin Musulunci a Gombe
Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

Pantami ya tuna haduwarsa da malamin a Nijar

Farfesa Pantami ya bayyana lokacin da ya hadu da shi a shekarar 2022 a Nijar, ya bayyana irin mu'amalar da ke tsakaninsu duba da dangantakarsu ta kai shekaru 32.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro ya jero malaman Musulunci 2 da ya kamata a cafke

Ya bayyana cewa sun yi rashin ɗaya daga cikin mafiya alheri a tsakaninsu, musamman wajen karatun Alƙur’ani da ba da labarai da darussan magabatanmu salihai.

Ya kara da cewa:

"Ya Allah, Ka gafarta wa Hafiz Aliyu Ladan, Ka ɗaukaka matsayinsa cikin waɗanda Ka shiryar, Ka sanya shi cikin sahun waɗanda suka gabace mu da kyautatawa, kuma Ka kula da iyalansa da ya bari a baya."

Babban malami ya rasu a Maiduguri

Mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin addinin Musulunci ya rasu a Maiduguri ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026 da muke ciki wanda ya tayar da hankulan jama'a.

Wani matashi, Ibn Maigana ya sanar da rasuwar malamin, yana bayyana shi a matsayin mashahurin malami da ya ilmantar tare da tasiri ga al'ummar Bolori.

Bayan rasuwarsa, jama'a sun ci gaba da yi masa addu'a, yayin da aka tuna gudummawarsa ga addini, ilimi da tarbiyyar al'umma a birnin Maiduguri da kewaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.