Abin da Kwankwaso Ya Ce kan INEC Bayan Taya Adeleke Murnar Tazarce a Osun
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani ga Gwamna Ademola Adeleke bayan ya sake lashe zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar
- Kwankwaso ya yaba wa al’ummar Osun saboda amfani da haƙƙinsu na zaɓe, yana mai cewa sakamakon ya nuna ƙarfin ikon jama’a
- Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya kuma yaba wa INEC, tare da kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaɓe mai gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana game da zaben jihar Osun.
Kwankwaso ya taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agustan shekarar 2026.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan Kano ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi 16 ga watan Agustan 2026.
Kwankwaso ya taya Adeleke murnar tazarce
Kwankwaso ya bayyana Adeleke a matsayin abokinsa, tare da yaba masa saboda samun nasara a zaɓen da aka fafata sosai.
Ya kuma taya al’ummar Osun murna saboda amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya da kuma sake tabbatar da abin da ya kira ikon zaɓin jama’a.
Ya ce:
“A matsayina na jagoran adawa kuma ɗan dimokuraɗiyya mai kishin ƙasa, ina yaba wa al’ummar Osun saboda amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya da kuma sake tabbatar da ikon zaɓin jama’a.”

Source: Original
Yabon da Kwankwaso ya yi ga INEC
Jigon NDC ya ce sakamakon zaɓen ya nuna muhimmancin yadda ’yan ƙasa ke shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya da kuma taka rawa wajen gudanar da zaɓe.
Ya ce zaɓen ya kasance abin tunatarwa cewa idan ’yan ƙasa suka ci gaba da sauke nauyin da ke kansu tare da bayyana ra’ayoyinsu, muradin jama’a zai yi nasara.
Kwankwaso ya kuma yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa yadda ta gudanar da zaɓen, yana kira ga duk masu ruwa da tsaki su ci gaba da tallafa wa zaɓe mai inganci, zaman lafiya da gaskiya.
Ya ce:
“Ina kuma yaba wa INEC bisa yadda ta gudanar da zaɓen, kuma ina ƙarfafa gwiwar duk masu ruwa da tsaki da su ci gaba da kiyaye ƙa’idojin zaɓe mai inganci, zaman lafiya da gaskiya.”
Ya ƙara da taya Adeleke da al’ummar Osun murnar sakamakon zaɓen da aka fitar wanda ya nuna tsantsar yadda aka ba al'umma dama.
“Ina sake taya Gwamna Adeleke da al’ummar Osun murna.”
- Cewar Rabiu Kwankwaso
Atiku ya taya Adeleke murnar tazarce
Mun ba ku labarin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya taya Gwamna Ademola Adeleke murnar sake lashe zaɓen gwamnan Osun.
INEC ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen, inda ya samu ƙuri’u 511,067, tare da nasara a ƙananan hukumomi 19.
Atiku ya ce nasarar Adeleke ta nuna zaɓin al’ummar Osun, yana yaba musu saboda yadda suka shiga zaɓen cikin kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng

