Raɗaɗin Faɗuwa: Yadda Ƴan APC Suka Yi wa Ɗan Jarida Dukan Tsiya a Rumfar Zaɓe

Raɗaɗin Faɗuwa: Yadda Ƴan APC Suka Yi wa Ɗan Jarida Dukan Tsiya a Rumfar Zaɓe

  • Wasu magoya bayan APC sun lakada wa ɗan jarida dukan yayin da yake aikin rahoto a zaɓen gwamnan jihar Osun
  • Lamarin ya faru a rumfar zaɓen ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, inda aka kama Oluwafemi, aka mare shi tare da kwace katin shaidarsa
  • ’Yan sanda sun shiga tsakani domin kare ɗan jaridar, amma daga baya wani maharin sanye da kayan jami’in tsaro ya kore shi da bulala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Wasu magoya bayan jam’iyyar APC sun kai hari kan wani ɗan jarida a zaɓen gwamnan da ake yi a Osun.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a mazabar dan takarar gwamnan APC, Bola Oyebamiji.

Yan APC sun ci zarafin ɗan jarida a rumfar zabe
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben Osun, Bola Oyebamiji da shugaban jam'iyyar, Nentawe Yilwatda a Osogbo. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Facebook

Dan jarida ya sha duka a rumfar zabe

An ce yan APC din yi wa Ayodele Oluwafemi, ɗan jaridar TheCable, mummunan duka yayin da yake aikin ɗaukar rahoto kan zaɓen.

Kara karanta wannan

EFCC ta kai wani mutum kotu kan zargin baba kere da N56m na kudin aikin hajji

Lamarin ya faru ne a rumfar zaɓen Bola Oyebamiji, ɗan takarar APC a zaɓen. Rumfar tana Gantry Sawmill, Ikire I, ƙaramar hukumar Irewole ta Osun.

Yayin da hasken rana ya fara dusashewa da misalin ƙarfe 6 na yamma, mazauna yankin suka kawo janareta da fitilun lantarki domin samar da haske da ba da damar ci gaba da kaɗa kuri’a.

Bayan an kunna janaretan, Oluwafemi ya ci gaba da aikinsa na rubuta abubuwan da ke faruwa.

Ba zato ba tsammani, wasu mutane biyu suka tunkare shi, suna tambayar dalilin da ya sa har yanzu yake rumfar da misalin ƙarfe 7 na dare.

Mtanen sun kama rigarsa, suka mare shi sau da dama, sannan suka kwace katin shaidarsa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ba shi.

An yi wa dan jarida dukan tsiya a rumfar zabe
Taswirar jihar Osun da jam'iyyar Accord ta lashe zaben gwamna. Hoto: Legit.
Source: Original

Ƴan sanda sun kawo dauki

Wasu mutane uku kuma sun shiga cikin harin, a lokacin da ake dukansa, mutanen sun ci gaba da tambayarsa abin da yake yi a rumfar zaɓen da misalin ƙarfe 7 na dare.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya gano shirin da APC ta yi wajen tattara sakamakon zaben Osun

A wani lokaci, jami’an ’yan sanda da ke rumfar zaɓen, waɗanda tun farko suka yi watsi da lamarin, daga bisani suka shiga tsakani domin kare shi daga ƙarin hari.

Oluwafemi ya ce:

“Da sauri na gudu domin neman mafaka a ɗaya daga cikin motocin ’yan sanda. Mutanen suka ci gaba da bina. Yayin da nake shirin shiga motar, ɗaya daga cikin jami’an ’yan sanda ya ture ni."

Duk da shiga tsakani da ’yan sandan suka yi, mutanen sun dage cewa Oluwafemi ya nuna musu katin shaidar kamfaninsa, kafin daga bisani su bar shi.

Jami’in dan sanda ya umarci ɗan jaridar da ya gaggauta barin rumfar, yana cewa kasancewarsa a wurin ya fusata wasu mutane.

Yayin da Oluwafemi ke ƙoƙarin samun nutsuwa da barin yankin, ɗaya daga cikin mutanen da suka kai masa hari, wanda ke sanye da kayan jami’in tsaro na kamfani mai zaman kansa, ya kore shi da bulala.

Yan daban sun tarwatsa masu zabe a Osun

An ji cewa an samu rikici a kada kuri’a a rumfar tsohon gwamnan Osun kuma tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Rahotanni sun ce ‘yan daban sun kori masu kada kuri’a daga rumfar, lamarin da ya haifar da fargaba tare da dagula tsarin zaben gwamnan.

Hukumar INEC da jami’an tsaro ba su bayyana cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da jiran matakan da za a dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.