An Shiga Tashin Hankali, Mai Gabatar da Shirye Shirye Ta Faɗi Ta Mutu a OGTV
- An shiga jimami a gidan talabijin mallakin gwamnatin jihar Ogun da Allah ya karɓi rayuwar mai gabatar da shirye-shirye tana shirin fara aiki
- An ruwaito cewa ƴar jaridar, Mrs. Bukola Agbakaizu ta yanke jiki ta faɗi a OGTV, kuma wani likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa da aka kai ta asibiti
- Kungiyar mata ƴan jarida (NAWOJ) reshen jihar Ogun ta yi alhinin wannan rashi tare da addu'ar Allah Ya gafartawa Marigayi Bukola Agbakaizu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Ogun, ta shiga cikin jimami a ranar Litinin bayan rasuwar wata ‘yar jarida mai aikin gabatar shirye-shirye, Mrs. Bukola Agbakaizu.
Fitacciyar ƴar jaridar ta rasu ne a ofis yayin da take shirin karɓar aikin rana a gidan talabijin na gwamnatin jihar Ogun da ke Abeokuta.

Asali: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa marigayiyar tsohuwar shugaba ce a kungiyar NUJ ta jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴar jarida ta mutu a OGTV
Rahoton da muka samu ya nuna cewa ƴar jaridar ta yanke jiki ta faɗi ne a daya daga cikin dakunan watsa shirye-shiryen Gidan Talabijin na Jihar Ogun (OGTV).
Likita a Asibitin Tarayya (FMC) da ke Idi-Aba, Abeokuta, ya tabbatar da rasuwarta bayan an garzaya da ita domin kulawar gaggawa.
Wani abokin aikinta a OGTV ya shaida cewa marigayiyar ba ta nuna wata alamar rashin lafiya ba kafin rasuwarta, yana mai cewa ta ƙariso wurin aiki ciki nishadi da shirin fara aikinta na rana.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa Mrs. Bukola Agbakaizu tana fama da ciwon hawan jini kuma likita ya ɗora ta a kan magunguna, rahoton Voice Of Nigeria.
Kungiyar NAWOJ ta miƙa sakon ta'aziyya
Ƙungiyar mata ‘yan jarida ta kasa (NAWOJ), reshen jihar Ogun, ta nuna matukar bakin cikinta kan rasuwar Agbakaizu, inda ta bayyana ta a matsayin mace mai sadaukarwa da kwazo a aikin jarida.
Shugabar NAWOJ ta jihar, Sekinat Salam, ta fitar da sanarwar ta’aziyya inda ta ce:
“Rasuwar Bukola Agbakaizu babban rashi ne da ke da ciwo. Lokacin da muke bukatar kwarewarta da jagorancinta, ita kuma ta riga mu gidan gaskiya.
"Za mu yi kewarta sosai saboda soyayyarta ga mutane, jajircewarta da kaunar aikin jarida.”
Ta kara da cewa, duk da cewa Agbakaizu ta rasu tana da shekaru 52, jajircewarta wajen hidima ga al’umma za su ci gaba da kasancewa a cikin zukatan mutane har abada.
“Muna addu’a Allah ya jikanta da rahama, ya kuma bai wa iyalanta ƙarfin zuciya da kariya daga Ubangiji Madaukaki. Ki huta lafiya, jaruma a fagen jarida,” in ji sanarwar.
Tsohon gwamna a Najeriya ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Bayelsa , Kyaftin ɗin sojan ruwa, Omoniyi Caleb Olubolade (mai ritaya), ya rasu yana da shekaru 70.
An ce Kyaftin Olubolade ya yanke jiki ya fadi yayin da yake wasan kwallon teburi a wani filin wasa da ke kusa da gidansa, a Apapa da ke jihar Legas.
Duk wani kokari na ceto rayuwar tsohon gwamnan ya ci tura, inda aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin sojojin ruwa na Obisesan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng