‘Addu’a Ma Ya Ishe Su’: Malami Ya Fadi Yadda Za a Kawo Karshen Boko Haram
- Wani Fasto Oliver Dashe na Maiduguri ya bukaci Kiristoci su kara dagewa da addu’a domin taimaka wajen murkushe Boko Haram
- Ya ce Borno ta samu zaman lafiya amma gwamnati da jama’a su ci gaba da kokarin tabbatar da cikakken nasara
- Bishop Dashe ya kuma bukaci gwamnati ta tarayya da jihohi su tallafa wa jami’an tsaro domin shiga dazuka da tsaunuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Faston Katolika na Maiduguri, Rabaran Oliver Dashe, ya yi kira ga Kiristoci da su kara dagewa wajen yin addu’a saboda matsalar tsaro.
Bishop Dashe ya ce addu’a na da karfin taimakawa wajen murkushe Boko Haram, amma ya jaddada cewa mutane da gwamnati ma dole su taka nasu rawa.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai bayan wani taron coci da aka gudanar a babban cocin St. Patrick da ke Maiduguri, babban birnin Borno, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Tsautsayi ya faɗa kan matar aure da 'ya'yanta 2 cikin dare, Allah ya musu rasuwa a Kaduna
Yadda matsalar Boko Haram ya shafi al'umma
Taron ya kasance wani bangare na bikin tunawa da tashin Budurwa Maryamu zuwa sama, wanda ke da muhimmanci a Cocin Katolika.
Bishop Dashe ya yaba da zaman lafiyar da Borno ta samu a 'yan shekarun nan bayan shafe fiye da shekaru 10 tana fama da tada kayar baya.
Ya ce duk da cewa addu’a na da muhimmanci wajen samun nasara, dole ne gwamnati da al’umma su ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar tsaro.
Fasto Dashe ya ce ranar bikin ta kasance muhimmiyar rana ga Cocin Katolika, yana mai bayyana irin muhimmancin da Budurwa Maryamu ke da shi a rayuwar mabiya addinin a Maiduguri.

Source: Original
Muhimmancin addu'a a yaki da rashin tsaro
Malamin ya ce ya shafe shekaru 17 yana matsayin bishop na Maiduguri, kuma ya danganta ci gaban rayuwarsa da addu’ar Budurwa Maryamu.
Da yake magana kan muhimmancin addu’a wajen yaki da rashin tsaro, bishop din ya bukaci Kiristoci su kasance cikin shiri ta hanyar dagewa wajen yin addu’a.
Ya ce:
“Ta bangaren addini, mun san cewa addu’a za ta murkushe Boko Haram. Amma ya kamata mu sani cewa yayin da muke addu’a, mutane ma dole su yi aikinsu.”
Ya kara da cewa Kiristoci su kasance cikin shiri, kuma daya daga cikin hanyoyin kasancewa cikin shiri shi ne dagewa wajen yin addu’a, cewar Vanguard.
Faston din ya ce zaman lafiyar da ake samu a Borno a yanzu na iya kasancewa sakamakon taimakon da yake cewa Budurwa Maryamu ta bayar.
Ya tuna cewa lokacin da rikicin Boko Haram ya fara kusan shekaru 17 da suka gabata, lamarin ya kasance mai tsanani sosai.
Sai dai bishop din ya bukaci gwamnati a matakan tarayya da jihohi ta dauki matakan da suka dace, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon bayan da suke bukata.
Boko Haram sun sace dalibai a Borno
A baya, an ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari da sanyin safiya a wasu makarantu da ke jihar Borno ta tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan
Duk da yi masu gorin tikitin Muslim Muslim, Kiristoci sun shirya abin alheri ga Tinubu
Tsagerun 'yan ta'addan sun kai farmakin ne bayan sun jira jami'an tsaron da ke aikin sintiri sun bar yankin.
Majiyoyi sun bayyana cewa ana fargabar 'yan ta'addan sun yi awon gaba da dalibai masu yawa zuwa cikin daji bayan kawo harin.
Asali: Legit.ng
