Tsautsayi Ya Fada kan Matar Aure da 'Ya'yanta 2 cikin Dare, Allah Ya Musu Rasuwa a Kaduna
- Wata mata mai shekara 35 da ’ya’yanta biyu sun mutu bayan wani gini da ake ginawa ya rufta kan gidansu a jihar Kaduna
- Yaran da suka mutu sun hada da Salisu mai shekara biyar a duniya da Muhammad mai watanni uku da haihuwa
- Makwabta sun yi kokarin ceto wadanda abin ya rutsa da su, amma sun fito da su bayan sun riga sun mutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Wata mata mai shekara 35, da 'ya'yanta biyu sun mutu bayan wani gini da ake ginawa ya rufta kan gidansu a unguwar Dan Mani da ke yankin Rigasa, jihar Kaduna.
Lamarin ya faru da misalin karfe 3:30 na dare ranar Juma’a a yankin Abuja Road, Kwanar Mai Dabino da ke Rigasa.

Source: Original
Mijin matar, Abubakar Abba Haruna, ya ce ba ya gida lokacin da lamarin ya faru, domin ya kwana a gidan dayar matarsa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya ce babbar diyarsa ce ta tashe shi ta hanyar kwankwasa masa kofa tare da sanar da shi cewa ginin ya rufta kan mahaifiyarsu.
"Na fito cikin firgici, na dauki babur dina na garzaya gida,” in ji Haruna.
Makwabta sun yi kokarin ceto su
Haruna ya ce lokacin da ya isa wurin, tuni makwabta suka fara kokarin ceto wadanda ginin ya rutsa da su daga cikin baraguzan ginin, sai dai lokacin da aka samu damar fito da su, duk sun riga sun mutu.
“Babu wanda ya nuna alamar rauni, domin ginin ne ya rufta kansu,” in ji shi.
Haruna ya bayyana sunan matarsa da ta rasu da Takiyatu, yayin da ’ya’yan biyu suka kasance Salisu mai shekara biyar da Muhammad, wanda ke da watanni uku kacal.
Magidancin ya rungumi kaddara
Haruna ya bayyana mutuwar iyalansa a matsayin wata babbar jarrabawa daga Allah, yana mai cewa babu abin da iyalan za su iya yi illa su hakura su yi addu’a ga wadanda suka rasu.
“Abin da ya faru daga Allah ne, don haka babu abin da zan iya yi illa yi musu addu’a. Allah Ya ji kan ta da yaran. Jarrabawa ce Allah Ya kawo mana. Abin da za mu iya yi shi ne mu yi hakuri,” in ji shi.
Mutanen Abuja Road sun shiga jimami
Shugaban al’ummar yankin Abuja Road, Kwanar Mai Dabino da ke Rigasa, Sani Ayuba, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ayuba ya ce mazauna yankin sun shiga cikin jimami sakamakon wannan mummunan lamari, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Ya bayyana cewa wata katanga daga wani gini da ake ginawa a makwabta ya rufta kan gidan da matar da ’ya’yanta suke barci, lamarin da ya binne su a karkashin baraguzan ginin.
Ginin makaranta ya rufta kan dalibai
Kun ji cewa ginin makarantar gwamnati ya rushe kan dalibai sakamakon ruwan sama mai ƙarfi, inda yara bakwai suka mutu, wasu 20 suka jikkata.
Mutanen yankin sun bayyana fushinsu tare da zargin cewa sun sha fadawa hukumomi irin matsalar ginin, amma ba a ɗauki mataki ba har iftila'in ya faru.
Asali: Legit.ng

