Naɗin Sarauta Ya Koma Jimami, Ɗan Banga Ya Bindige Matashi Har Lahira a Borno

Naɗin Sarauta Ya Koma Jimami, Ɗan Banga Ya Bindige Matashi Har Lahira a Borno

  • An harbe wani matashi da bindiga a lokacin bikin naɗin sarauta a Gwoza, jihar Borno. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar
  • Yusuf Ahmadu ya harbe Isa Ali da gangan lokacin da ya karɓi bindiga daga wani jami'in sa-kai Buba Hamman a wurin bikin
  • An kai wanda aka harba asibitin Gwoza, likitoci suka tabbatar da mutuwarsa inda yan sanda sun kama Ahmadu da Hamman don bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gwoza, Borno - An shiga wani irin yanayi a jihar Borno bayan hallaka wani matashin da bindiga yayin taro.

An tabbatar da kisan matashin ne a yau Lahadi 11 ga watan Mayun 2025 yayin nadin sarauta.

An bindige matashi a Borno
An bindige matashin yayin nadin sarauta a Borno. Hoto: Legit.
Asali: Original

Wannan na cikin wata sanarwa da shafin Zagazola Makama ya tabbatar a manhajar X a yau Lahadi 11 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Borno: Matsalolin tsaro a karamar hukumar Gwoza

Gwoza dai na daga cikin garuruwa da ke fama da matsalolin tsaro a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas wanda ya daidaita harkokin kasuwanci.

Yan ta'addan Boko Haram sun sha fafatawa da dakarun sojoji wanda ake yawan samun rasa rayuka da dukiyoyin al'umma.

A kwanan nan ma, Boko Haram sun farmaki dakarun 'Operation Hadin Kai' a kauyen Izge da ke cikin dajin Sambisa a karamar hukumar.

A yayin harin an hallaka aƙalla sojoji guda biyu, yayin da suka samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa.

An harbe matashi a Borno bisa kuskure
Dan banga ya harba matashin yayin nadin sarauta a Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Twitter

Borno: Matashi ya rasa ransa bayan harbin bindiga

Rahoton ya ce matashi ya rasa ransa yayin bikin naɗin sarauta a Gwoza, jihar Borno.

Lamarin ya faru a jiya ranar Asabar 10 ga watan Mayun 2025 bayan dan banga ya harba bindiga ba da gangan ba.

Majiyoyi sun shaida wa cewa Buba Hamman, jami'in sa-kai, ya mika bindigar da ke ɗauke da harsashi ga Yusuf Ahmadu.

Yusuf Ahmadu ya harbi Isa Ali mai shekara 18 a ƙirji bisa kuskure yayin da yake rike da bindigar a wurin taron.

Halin da ake ciki a yanzu

An garzaya da Isa Ali zuwa babban Asibitin Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa a lokacin da aka kai shi.

Jami’an tsaro sun isa wurin da gaggawa, suka kwato bindigar, sannan suka kama Ahmadu da Hamman don ci gaba da bincike.

Rundunar ƴan sandan Borno ta ce har yanzu ba a tantance dalilin faruwar lamarin ba yayin da ake ci gaba da bincike.

Fasto ya bindige jami'an hukumar NIS a Abuja

A baya, kun ji cewa wasu jami'an shige da fice biyu sun jikkata bayan wani mutum da ake kira Fasto Darlington ya harbe su bisa kuskuren zargin su 'yan fashi ne.

An ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a ranar Asabar 10 ga watan Mayun 2025 a Sabon Iddo, lokacin da jami’an suke zagayen sintiri a yankin.

Tuni aka garzaya da su asibitin Rundunar Sojin Sama da ke Abuja, yayin da 'yan sanda ke neman Fasto Darlington wanda ya tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.