Zaben Osun: Kananan Hukumomin da Gwamna Adeleke da Dan Takarar APC Suka Lashe
- Ademola Adeleke na Accord Party ya lashe kananan hukumomi masu yawa cikin 30, yayin da Bola Oyebamiji na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11
- Gwamna Adeleke ya samu jimillar kuri’u 511,067, inda ya doke Oyebamiji da kuri’u 444,815, tazarar kuri’u 66,252.
- Najeem Salaam na ADC ya zo na uku da kuri’u 17,180, yayin da ake jiran sanarwar karshe ta INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Osogbo, Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party ya lashe kananan hukumomi m19 cikin 30 a zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar.
Sakamakon da aka tattara daga cibiyoyin tattara sakamako na kananan hukumomin ya nuna cewa Adeleke ya samu jimillar kuri’u 511,067.

Source: Twitter
Dan takarar jam'iyyar APC, Munirudeen Bola Oyebamiji, ya zo na biyu da kuri’u 444,815, yayin da dan takarar ADC, Najeem Salaam, ya kare a matsayi na uku da kuri’u 17,180, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Adeleke Ya doke Oyebamiji da kuri’u 66,252
Jimillar sakamakon kananan hukumomi 30 ta sanya Adeleke a gaba da Oyebamiji da tazarar kuri’u 66,252.
Gwamna Adeleke ya samu nasara a Boluwaduro, Ede South, Ife North, Ilesa West, Ifedayo, Ife Central, Orolu, Osogbo, Oriade da Odo-Otin.
Sauran kananan hukumomin da ya lashe sun hada da Ife East, Ifelodun, Iwo, Ede North, Ila, Aiyedire, Egbedore, Ayedaade da Ejigbo.
APC ta lashe kananan hukumomi 11
A bangaren APC, Bola Oyebamiji ya samu nasara a kananan hukumomi 11 na jihar Osun, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Kananan hukumomin da APC ta lashe su ne Ilesa East, Boripe, Irepodun, Obokun, Atakunmosa West, Irewole, Atakunmosa East, Isokan, Ola Oluwa, Ife South da Olorunda.
Wannan ya nuna cewa duk da nasarar Adeleke a mafi yawan kananan hukumomi, APC ta samu gagarumar nasara a wasu yankunan jihar.
INEC na shirin sanar da wanda ya lashe zaben
Zaben ya samu halartar ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa da dama, yayin da Adeleke ke neman sake komawa kan mulki a karkashin Accord Party, sannan Oyebamiji ke wakiltar APC.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ce ta gudanar da zaben a fadin Jihar Osun, sannan aka tattara sakamakon daga kananan hukumomi 30.
Yayin da sakamakon ke nuna cewa Adeleke ya lashe kananan hukumomi 19, yayin da Oyebamiji ya lashe 11, sanarwar karshe ta INEC ce za ta tabbatar da wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Osun a hukumance.

Source: Twitter
Dan takarar APC ya sha da kyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin gwamnan jihar Osun na jam’iyyar APC, Injiniya Kayode Adereti, ya sha da kyar a sakamakon zaben rumfarsa, inda ya samu nasara da tazarar ƙuri’u shida kacal.
Adereti, wanda ya jefa ƙuri’arsa a Ward 03, Unit 011, Ilare, a ƙaramar hukumar Ife Central, ya samu ƙuri’u 132 na APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu ƙuri’u 126.
Asali: Legit.ng

