"So Ya Zama Ajali": Matashi Ya 'Mutu' a Gidan Budurwarsa daga zuwa Taɗi a Kano
- Jami'an yan sanda sun cafke wani matashin ɗan shekara 25, Mansur Umar bisa zargin kisan saurayin kanwarsa, Firdausi Umar a jihar Kano
- Mai magana da yawun ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Mansur ya kashe saurayin ne a lokacin da ya je taɗi gidansu ranar Juma'a
- Ya ce Mansur ya bugawa saurayin mai suna, Suleiman Musa sanda a kai, kuma bayan kai shi asibiti rai ya yi halinsa ranar Asabar da ta wuce
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna, Mansur Umar, bisa zargin kashe saurayin ‘yar uwarsa a Kauyen Kunya, karamar hukumar Minjibir.
Matashin ya hallaka saurayin ne a lokacin da ya je taɗi wajen kanwarsa a gidansu ranar Juma'a da ta gabata.

Asali: Facebook
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe matashi daga zuwa taɗi
Kakakin ƴan sandan ya ce lamarin ya faru ne da misalin 9:30 na dare ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025.
Abdullahi Kiyawa ya ce mamacin, Sulaiman Musa, wanda shi ma dan shekara 25 ne daga Kauyen Goda, ya je gidansu budurwarsa, Fiddausi Umar domin ya ziyarce ta kamar yadda masoya suka saba.
Ya ƙara da cewa yayin wannan ziyara ne Mansur Umar, yayan Fiddausi, ya narka wa Sulaiman sanda a kai, lamarin da ya jikkata shi matuka.
Matashin ya rasu a asibitin Murtala
"An garzaya da shi asibitin Kunya, daga bisani aka tura shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
"Duk da kokarin da likitoci suka yi na ceto rayuwar saurayin, sun tabbatar da cewa Allah ya masa rasuwa da misalin 12:50 na daren ranar Asabar.
- Abdullahi Haruna Kiyawa.

Asali: Original
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Rundunar ƴan sanda ta ce tuni dakarunta suka kamo wanda ake zargi, yayin da Jami'an Sashin Binciken Manyan Laifuka (CID) ke ci gaba da gudanar da bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin, yana mai yin kira da a kaurace wa daukar doka a hannu da kuma rungumar sulhu da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci al’umma su kasance masu fahimta da kai rahoton duk wani abu da suka gani ba su yarda da shi ba, don tabbatar da tsaro da bin doka da oda a fadin jihar Kano.
Matashi ya auri wacce ta girme shi a Kano
A wani labarin, kun ji cewa wani matashin ɗan shekara 25, Mustapha PK ya angonce da wacce ta ɗara shi shekaru, Aunty Samira, yar shekara 39 a jihar Kano.
A cewar angon, ya auri Samira ne ba don kwaɗayin abin hannunta ko wani abu makamancin haka ba domin shi ma Allah Ya rufa masa asiri daidai gwargwado.
Mustapha PK ya bayyana cewa irin yawan kyautatawar da Anty Samira ke masa ya sa sonta ya mamaye ilahirin zuciyarsa har ta kai ya fara jin yana son zaman aure da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng