Bayan An Gama Jere, Mummunar Gobara Ta Babbake Dakin Sabuwar Amarya a Zamfara
- Wata mummunar gobara da ta tashi ta lalata gidan wata sabuwar amarya a Zamfara, kwana daya da kammala yin jeren kayanta
- Wani ganau ya shaida cewa amaryar da kawayenta sun isa gidan bayan samun labarin gobarar, inda suka barke da kukan bakin ciki
- An ce gobarar ta fara ne daga gidan wata tsohuwa, wacce ta ce ta ji lokacin da wani abu ya fashe a rufin dakinta, sannan wutar ta shi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Wata mummunar gobara ta ta lalata gidan wata sabuwar amarya ana saura kwana ɗaya a daura aurenta a jihar Zamfara.
An ce gobarar ta lalata gidan amarya ne tare da wasu gidaje shida, inda ɗaya daga cikinsu na ma’aikacin hukumar kashe gobara ta jihar ne.

Asali: Original
Gobara ta babbake gidaje 7 a Zamfara
Wani ganau, Malan Dan Sokoto, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:40 na safiya, kuma matan da ke gidajen ne suka yi kururuwar neman taimako, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malan Dan Sokoto ya ce gobarar ta shafi gidan wata Hajiya, wadda ta kasance ita ce dattijuwa a gidajen da abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa:
“Lokacin da muka je fitar da tsohuwar daga cikin ɗakinta, inda ake zargin daga nan gobarar ta fara tashi, mun tarar da wutar tana ci gadan-gadan.
"Ko da muka yi kokarin kashe gobarar ta hanyar zuba mata ruwa, sai wutar ta kara tashi sosai, kamar muna kara watsa mata fetur ne.”
Lokacin da aka tambaye ta game da musabbabin gobarar, tsohuwar ta ce ta ji lokacin da wutar ta ke ci a rufin dakinta, amma ba ta iya yin komai ba.
Motar 'yan kwana-kwana ta samu matsala
Hajiya ta shaida cewa:
“Daga rufin dakina ta fara. Ko da yake ba zan iya gano ainihin musabbabin tashin wutar ba amma na ji wani sauti da ke nuna cewa wani abu ne ya fashe a cikin rufin ɗakin."
Maƙwabtan waɗanda abin ya shafa sun ce an sanar da hukumar kashe gobara kuma sun iso da wuri amma saboda matsaloli na nau'ra, sai motocin kashe wutar suka ƙi aiki yadda ya kamata.
Sun shaida cewa sama da awa guda, jami’an kashe gobarar suna ƙoƙarin gyara matsalar, lamarin da ya sa gobarar ta yadu a sauran gidaje.
Malan Dan Sokoto ya bayyana cewa:
“Gobarar ta lalata gidaje bakwai kuma ɗayansu na ma’aikacin hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara ne.”

Asali: Original
Dakin sabuwar amarya ya babbake gaba daya
An rahoto cewa amaryar da aka kammala yin jeren kayanta, da zummar kai ta dakinta washe gari, ta isa gidan bayan jin labarin gobarar tare da kawayenta, inda suka kama kuka.
Wata kawar amaryar da aka yi magana da ita, ta shaida cewa:
“Jiya jiyan nan muka kawo dukkanin kayanta muka jera komai da nufin ta more su a rayuwar aurenta da za daura gobe, sai ga shi gobarar ta lalata komai gaba ɗaya.”
Babban sakataren hukumar kashe gobara ta Zamfara, Bello Sani, ya tabbatar da cewa ma’aikatansu sun kai dauki da wuri kuma gwamnatin jihar ta farfaɗo da tashoshin kashe gobara da yawa da suka lalace.
Amarya ta mutu a cikin gobara kwanaki 3 da aure
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata amarya mai suna Nana ta gamu da ajalinta sakamakon wata gobara da ta tashi a gidanta.
Kawar amaryar mai suna Safiyya Idris, wacce ta ba da labarin ta ce gobarar ta hallaka Nana ne kwanaki uku kacal da tarewarta da angonta Jabeer.
Safiyya ta bayyana cewa tsananin gobarar ta kai ga cewa komai a gidan ya kone kurmus, amma ta shaida cewa mijin Nana ya tsira da ransa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng