Tirkashi: An Gwabza Tsakanin Davido da Dan Majalisa kan Zaben Gwamnan Osun

Tirkashi: An Gwabza Tsakanin Davido da Dan Majalisa kan Zaben Gwamnan Osun

  • Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikeja a Legas, James Faleke, ya musanta yunkurin yin tasiri kan INEC domin sauya sakamakon zaben gwamnan jihar Osun
  • James Faleke ya ce ya je Osun ne domin mara wa dan takarar APC, Bola Oyebamiji, baya, yayin da Davido ya goyi bayan kawunsa, Ademola Adeleke
  • Gwamna Ademola Adeleke dai ya lashe zaben gwamnan Osun da kuri’u 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ikeja a Legas, James Faleke, ya yi wa Davido martani kan zaben gwamnan Osun.

James Faleke ya musanta zargin yunkurin yin tasiri kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin sauya sakamakon zaben gwamnan jihar Osun.

Faleke ya yi wa Davido martani
Dan majalisar wakilai, James Faleke da mawaki Davido Hoto: @honfaleke, @davido
Source: Twitter

Faleke, wanda ya mara wa dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Oyebamiji, baya, ya yi wannan karin bayani ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Davido ya yi magana kan nasarar kawunsa, ya cika da murna

Me Davido ya ce kan dan majalisa?

Dan majalisar ya yi bayanin ne bayan wani tsokaci da mawakin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi.

A lokacin da ake tattara sakamakon zaben a Osogbo ranar Asabar, Davido ya zargi Faleke da matsa wa INEC lamba domin sauya sakamakon zaben.

“Hon. James Faleke, ka daina matsa wa INEC lamba domin sauya sakamakon zaben Osun. Ka mutunta zabin al’ummar Osun. Ba ma son Oyetola da AMBO,” in ji Davido.

Faleke ya mayar da martani

Da yake mayar da martani, Faleke ya ce zuwansa jihar Osun shi ne domin mara wa dan takarar jam’iyyarsa baya, yayin da ya bayyana cewa Davido ya goyi bayan kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya tsaya takara karkashin jam’iyyar Accord.

“Na zo Osun ne domin mara wa dan takarar jam’iyyata baya, yayin da kai ka goyi bayan jam’iyyar kawunka (Accord). INEC hukuma ce da ni ko wani mutum ba zai iya yin tasiri a kanta ba,”

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Gwamna Adeleke ya yi magana kan nasararsa, ya aika sako ga Tinubu

"Ban taba yin tasiri ko magudin zabe a baya ba, kuma ba na shirin fara yin hakan yanzu. Ka fuskanci wakarka, mu kuma mu fuskanci tamu siyasar.” In ji shi.

Faleke ya taya Adeleke murna

Bayan da INEC ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben, Faleke ya sake wallafa wani sako inda ya taya gwamnan murnar lashe wa’adin mulki na biyu.

Ya kuma yaba wa Oyebamiji kan abin da ya bayyana a matsayin “kyakkyawan kokari”, tare da yabawa dan takarar na APC kan jajircewarsa da nuna kyakkyawar dabi’a a lokacin gudanar da zaben.

Faleke ya kuma bayyana zaben a matsayin shaida cewa dimokuradiyya na ci gaba da kafuwa a Najeriya, tare da yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abin da ya kira jajircewarta wajen tabbatar da dabi’un dimokuradiyya.

Ya kuma yabawa INEC kan yadda ta gudanar da zaben, da jami’an tsaro kan tabbatar da abin da ya bayyana a matsayin tsari mai zaman lafiya da lumana.

James Faleke ya taya Adeleke murna
James Faleke na jam'iyyar APC Hoto: @honfaleke
Source: Twitter

Kwankwaso ya taya Adeleke murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci kan zaben gwamnan jihar Osun.

Kankwaso ya taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agustan shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng