Zance Ya Kare, INEC Ta Fara Dora Sakamakon Zaben Gwamnan Osun a Shafin IReV
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta far dora sakamakon zaben gwamnan jihar Osun a shafinta na yanar gizo (IReV)
- Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa zuwa yanzu, INEC ta wallafa sakamakon rumfunan zaɓe 1,011 cikin 3,763 a shafinta na IReV
- Sakamakon da aka dora a shafin INEC ya kai kashi 26.87 cikin 100 na jimillar sakamakon da ake jira daga rumfunan zaben Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara dora sakamakon zaben gwamnan Osun a shafinta na tattara sakamako watau IReV.
Wannan na zuwa ne bayan an kammala kada kuri'u tare da kidaya wa a zaben gwamnan jihar Osun, wanda ya gudana yau Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026.

Source: Facebook
INEC ta fara dora sakamako a IReV

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Gwamna ya gano shirin da APC ta yi wajen tattara sakamakon zaben Osun
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kawo yanzu, INEC ta wallafa sama da kashi 25 cikin 100 na sakamakon zaɓen gwamnan jihar Osun a shafinta na IReV.
An fara ɗoraa sakamakon ne jim kaɗan bayan kammala kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe da dama a faɗin jihar, bayan rufe lokacin kaɗa ƙuri’ar.
Tun farko dai, INEC ta sanya ƙarfe 2:30 na rana a matsayin lokacin rufe zaɓen a kowace mazaba.
Sakamakon rumfunan 1,011 ya bayyana
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, an ɗora sakamakon rumfunan zaɓe 1,011 cikin rumfunan 3,763 da ke jihar Osun a shafin IReV, kimanin kashi 26.87 cikin 100 na jimillar sakamakon da ake sa ran za a wallafa.
Sai dai a rahoton Daily Trust, INEC ta dora sakamakon rumfunan zabe 1,517 daga cikin jimillar 3,763, watau kashi 40.31 cikin ɗari.
Wannan ci gaba ya nuna fara tura sakamakon rumfunan zaɓe ta hanyar na’ura tare da bai wa jama’a damar kallon sakamakon yayin da jami’an zaɓe ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.

Source: Facebook
IReV na ƙara bayyana gaskiya
Shafin IReV na bai wa jama’a da sauran masu ruwa da tsaki musamman masu sanya ido kan zabe damar duba sakamakon da aka wallafa daga rumfunan zaɓe.
Hakan na taimakawa wajen ƙara nuna gaskiya a tsarin zaɓe yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon daga rumfunan zaɓe zuwa matakan da suka dace.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun na kokarin tazarce a kan mulki karkashin inuwar jam'iyyar Accord, yayin da yan takarar jam'iyyun hamayya ke yunkurin kayar da shi.
Gwamna Adeleke ya zargi APC
Kun ji cewa gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya zargi APC da shirin kai sakamakon zaɓe kai tsaye zuwa cibiyar tattarawa maimakon bin tsarinNda aka tanada.
Adeleke ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe ta 9, Ward 2, a ƙaramar hukumar Ede North.
A cewarsa, hakan zai kauce wa tsarin da ya kamata a bi daga rumfunan zaɓe zuwa mazabu sannan zuwa ƙananan hukumomi kafin a kaiBsakamakon cibiyar tattara sakamakon.
Asali: Legit.ng
