"An Yi Babban Rashi": Mahaifin Tsohon Gwamnan Kaduna kuma Basarake Ya Rasu
- Allah ya yi wa Turakin Dawakin Zazzau, Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero rasuwa
- Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigayin, wanda ya bayyana a matsayin dattijon arziki
- Uba Sani ya ce marigayin, Turakin Dawakin Zazzau mutum ne mai addini wanda ya taimaki al'aumma, yana mai cewa masarautar Zazzau ta yi babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zaria, jihar Kaduna - Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya riga mu gidan gaskiya.
Gwamnan jihar Kaduna mai ci, Malam Uba Sani ne ya tabbatar da rasuwar Ramalan Yero, Turakin Dawakin Zazzau yau Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025.

Asali: Twitter
Gwamna Uba Sani ya kuma miƙa sakon ta'aziyya da alhinin rasuwar mahaifin tsohon gwamnan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X watau Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uba Sani ya yi alhinin rashin Ramalan Yero
Sanata Uba Sani ya bayyana jimami da kaɗuwa bisa wannan babban rashi, inda ya ambaci wasu daga cikin kyawawan halayen marigayin.
A sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 12 ga Mayu, 2025, Gwamna Uba Sani ya ce ya samu labarin rasuwar marigayin da “zuciya mai nauyi amma da godiya ga Allah (SWT)”.
Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai daraja a al’ada, addini da kuma matsayin dattijo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima da kyakkyawan shugabanci.
Marigayi Ramalan Yero shi ke riƙe da sarautar Turakin Dawakin Zazzau kafin Allah ya karɓi rayuwarsa.
Gwamnan Kaduna ya mika sakon ta'aziyya
"Alhaji Ramalan Yero ya kasance basarake mai daraja, shi ke eiƙe da sarautar Turakin Dawakin Zazzau.
"Raasuwarsa babba rashi ne ga Masarautar Zazzau domin ta yi rashin murya mai hikima, Jihar Kaduna ta yi rashin dattijo, kuma al’ummar Musulmi sun yi rashin ginshiki mai ƙarfi kuma jagora."
- In ji Gwamna Uba Sani.
Uba Sani ya yi addu'ar Allah gafarta masa
Gwamna Uba Sani ya yi addu’ar Allah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya sa shi a cikin Aljannatul Firdaus.
Har ila yau, Gwamnan Kaduna ya yi wa iyalan marigayin addu'a da fatan Allah Ya ba su juriya da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.
Alhaji Ramalan Yero ya rasu ne bayan shafe tsawon lokaci yana yi wa al'umma hidima kuma yana daga cikin fitattun dattawan jihar da suka taka rawar gani a fannonin zamantakewa da addini.
Ɗaya daga cikin ƴaƴansa, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, ya riƙe kujerar gwamnan Kaduna daga 2012 zuwa 2015.
Tsohon ɗan takarar gwamna ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Kano, Abdulkadir Yusuf Guɗe ya riga mu gidan gasƙiya yana da shekara 63 a duniya.
Abdulkadir Guɗe shi ne tsohon Sakataren Kungiyar NRO, masu fafutukar kawo ci gaba a Arewacin Najeriya a lokacin da yake raye.
Rahotannin sun tabbatar da cewa Abdulkadir Yusuf Guɗe ya rasu da safiyar ranar Juma’a bayan doguwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.
Asali: Legit.ng