Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Gwamna kuma Tsohon Minista Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Gwamna kuma Tsohon Minista Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon gwamnan Bayelsa, Kyaftin Omoniyi Olubolade, ya rasu yana da shekaru 70 a Legas, bayan ya faɗi yayin wasan ƙwallon teburi
  • 'Ya'yansa sun tabbatar da rasuwarsa a ranar Lahadi, 11 ga Mayu, yayin da suka ce za su sanar da shirye-shiryen jana'izarsa nan gaba
  • An ce Kyaftin Omoniyi Olubolade ya rike mukamin minista a ma'aikatu uku a lokacin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Kyaftin ɗin sojan ruwa, Omoniyi Caleb Olubolade (mai ritaya), ya rasu yana da shekaru 70 a ranar 11 ga Mayu, 2025.

An ce Kyaftin Olubolade ya yanke jiki ya fadi yayin da yake wasan kwallon teburi a wani filin wasa da ke kusa da gidansa, a Apapa, Legas.

Kyaftin Olubolade, tsohon gwamnan Rivers ya rasu
Kyaftin ɗin sojan ruwa, Omoniyi Caleb Olubolade (mai ritaya), ya rasu. Hoto: @iLoveAyomoses
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan Bayelsa ya rasu

Rahoton The Nation ya nuna cewa duk wani kokari na ceto rayuwar tsohon gwamnan ya ci tura, inda aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin sojan ruwa na Obisesan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane a shafin X sun yi jimamin rasuwar Olubolade, wanda suka kira da "jarumi mai kishin ƙasa" da kuma "mai son ci gaban al'umma" saboda ayyukansa a fannonin soja da siyasa.

'Ya'yansa, Oluwayemisi Akinadewo da Dayo Olubolade, sun tabbatar da rasuwarsa, kuma sun sanar da cewa za a bayyana shirye-shiryen jana'izarsa nan gaba.

Rasuwarsa babban rashi ne ga Najeriya, musamman ga jihohin Ekiti da Bayelsa, inda ya bar abubuwan tunawa na sadaukarwa, jagoranci na gari da kuma ci gaban al'umma.

Wanene Kyaftin Omoniyi Caleb Olubolade?

An haifi Kyaftin Omoniyi Caleb Olubolade a ranar 30 ga Nuwamba, 1954, a Ipoti-Ekiti, jihar Ekiti, kamar yadda bayani daga shafin WikiPedia ya nuna.

Ya shiga aikin sojan ruwan Najeriya a shekarar 1974 bayan ya kammala karatunsa a kwalejin horar da sojojin ruwa ta Britannia Royal da ke Burtaniya a 1975 da kuma kwalejin injiniya ta sojan ruwa a Indiya a 1979.

Daga ranar 27 ga Yuni, 1997, zuwa 9 ga Yuli, 1998, Olubolade ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Bayelsa a ƙarƙashin mulkin Janar Sani Abacha.

A wannan lokacin, ya kafa majalisar al'adu da fasaha ta jihar Bayelsa, wadda ta zama muhimmiyar ginshiƙi ga ci gaban al'ummar yankin.

Kyaftin Olubolade, tsohon ministan Najeriya ya rasu
Kyaftin ɗin sojan ruwa, Omoniyi Caleb Olubolade (mai ritaya), ya rasu. Hoto: @iLoveAyomoses
Asali: Twitter

Jonathan ya nada Kyaftin Olubolade minista

Bayan ya yi ritaya daga aikin sojan ruwa a shekarar 1999, Olubolade ya ci gaba da bayar da gudummawa a siyasance.

A zamanin Shugaba Goodluck Jonathan, ya riƙe muƙamai daban-daban kamar ministan ayyuka na musamman da ministan babban birnin tarayya (FCT).

Daga cikin mukaman da ya rike a majalisar FEC lokacin da Jonathan ya ke ofis har da ministan harkokin 'yan sanda.

A cikin Disamba 2024, aka yi bikin cikarsa shekaru 70 da haihuwa a Yenagoa, inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Gwamna Douye Diri suka halarci taron.

Tsohon gwamnan Oyo, Olunloyo ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jihar Oyo ta yi babban rashi yayin da aka samu labarin rasuwar tsohon gwamnan jihar, Dr. Omololu Olunloyo.

Dr. Olunloyo, wanda ya taɓa zama shugaban farko na kwalejin fasaha ta Ibadan, ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 6 ga Afrilun 2025.

Marigayin ya rasu ne kwanaki kaɗan kafin ya cika shekaru 90 a duniya, kuma kafin rasuwarsa, ya riƙe muƙamai daban-daban ciki har da na sarautar Balogun na Oyo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.