Malamin Addini Ya Tsere bayan Kuskuren Harbin Jami’an Shige da Fice 2 a Abuja

Malamin Addini Ya Tsere bayan Kuskuren Harbin Jami’an Shige da Fice 2 a Abuja

  • Jami’an shige da fice biyu sun jikkata bayan wani mutum da ake kira Fasto Darlington ya harbe su bisa kuskuren zargin su 'yan fashi ne
  • Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a Sabon Iddo, lokacin da jami’an suke zagayen sintiri a yankin
  • An garzaya da su asibitin Rundunar Sojin Sama da ke Abuja, yayin da 'yan sanda ke neman Fasto Darlington wanda ya tsere

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani abin takaici ya faru a Abuja inda wani 'Fasto' ya yi kuskuren harbin jami'an tsaron Najeriya.

An ce Faston ya yi harbi ne a bisa kuskure saboda yana tunanin ƴan fashi ne suka zo sata a yankin da yake.

Wani Fasto ya harbi jami'an shige da fice
Fasto ya harbe wasu jami'an shige da fice 2 a Abuja. Hoto: Nigeria Immigration Services, Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Rahoton Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a shafin X da ranar yau Lahadi 11 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan sanda ya harbi jami'ar hukumar NIS

Hakan na zuwa bayan makamancin haka ya faru a jihar Niger inda dan sanda ya dirkawa jami'ar shige da fice bindiga yayin arangama.

Wata jami’in shige da fice, Christian Oladimeji ta gamu da tsautsayi bayan yan sanda sun dirka mata harbi.

An ce jami'ar ta jikkata sakamakon harbin da ‘yan sanda suka yi yayin da suka fuskanci farmaki daga wasu bata-gari a birnin Minna na jihar Niger.

Yan sanda sun ce sun yi kokarin kwato kayan da ake zargi an sata, amma wasu ma’aikata da bata-gari suka kai musu hari suka lalata motarsu.

Fasto ya harbi jami'an NIS a Abuja
Ana neman Fasto bayan harbin jami'an NIS a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

An harbi jami'na hukumar NIS 2 a Abuja

Majiyar ta ce jami’an shige da fice biyu sun jikkata a unguwar Sabon Iddo da ke Abuja a daren Juma’a.

Hakan ya biyo bayan wani Fasto Darlington ya yi harbe bisa kuskuren zargin su ’yan fashi ne.

Wata majiya daga ‘yan sanda ya shaida cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na dare, lokacin da jami’an Oyomide Zion da Hakeem Mashood ke sintiri.

A cewar majiyar ‘yan sanda, da misalin ƙarfe 11:40 na dare, shugaban yan sanda a Iddo ya samu kira na gaggawa kuma ya tura jami’an sintiri wurin.

Da suka isa, wani jami’in shige da fice, Uduk James, ya shaida musu cewa abokan aikinsa sun samu rauni.

An garzaya da su asibitin Sojin Sama da ke birnin Abuja domin ba su kulawar gaggawa.

Majiyoyin ‘yan sanda sun ce an kara kaimi wajen nemo Fasto Darlington wanda ake zargi kuma ya tsere daga wurin bayan harbin.

Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban NIS

Kun ji cewa yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sake yin wata ta'asa a babban birnin tarayya Abuja.

Miyagun sun hallaka tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) a safiyar ranar Talata, 4 ga watan Maris 2025.

David Shikfu Parradang ya rasa ransa ne bayan ƴan bindigan sun bi sahunsa lokacin da ya ciro kuɗi daga banki a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.