Daga Hawa Karaga, Gwamna Ya Sa an Cafke Sarki da Fadawansa kan Naɗa Kansa a Sarauta
- Rundunar 'yan sanda ta kama sabon 'Sarkin' Ijare, Oba Adekolajo Aladeseyi, da wasu mutane hudu bisa zargin nada kansa ba bisa ka'ida ba
- Kakakin gidan sarauta ya ce an tilasta wa masu nada sarauta su kaddamar da nadin ne da karfin bindiga da karfe 2:30 na tsakar dare
- Kwamishinan 'yan sanda ya bayyana nadin a matsayin na bogi, yana mai cewa hakan zai iya haddasa rikici da tabarbarewar doka a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Basarake ya jefa kansa a matsala wanda ya jawo gwamnatin jihar Ondo ta umarci cafke shi saboda wasu zarge-zarge da ya shafi nadin sarauta.
An kama sabon Sarkin Ijare da ke karamar hukumar Ifedore, Oba Adekolajo Aladeseyi, Okilorigbokun II bisa nada kansa ba bisa ka’ida ba.

Asali: Twitter
An kama 'Sarki' da fadawansa a Ondo
An cafke Oba Aladeseyi da wasu masu sarauta hudu da yammacin Laraba 7 ga watan Mayun 2025 bisa umarnin gwamnatin jihar Ondo, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nada Sarkin ne ranar 17 ga Afrilu, 2025, kuma ya kamata ya fara shirye-shiryen nadin gargajiya na tsawon kwana 30 kafin aka kama shi.
Al’ummar Ijare ba su da Sarki tun shekarar 2011 bayan rasuwar Oba Adebamigbe Oluwagbemigun.
Duk da kokarin nada sabon Sarki ya ci tura saboda rikici tsakanin gidajen sarauta da shari'o'in da ke gaban kotu.

Asali: Original
Sarauta: An tura koke ga gwamnan jihar Ondo
Amma Aarinmo na Ijare, shugaban gidan Sejeokun, Cif Oluwole Oni, ya rubuta koke ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Ya ce an tilasta wa masu nada sarauta da bindiga su gudanar da nadin da misalin karfe 2:30 na dare.
Ya gargadi cewa za a fada cikin rikici idan aka bar wannan nadin ya ci gaba da kasancewa a haka ba tare da ɗaukar mataki ba.
Martanin yan sanda kan lamarin a Ondo
Kwamishinan ’yan sanda na Ondo, Wilfred Afolabi, ya tabbatar da kama Sarkin, yana mai bayyana nadin a matsayin na bogi da damfara.
Ya ce:
“Akwai hatsarin rikici a cikin al’umma, an tilasta wa wasu masu nadi su halarci nadin, wannan abu bai dace ba.
“Irin hakan na iya haddasa rikicin al’umma, zai iya janyo tabarbarewar doka da oda, wannan ya zama izina ga wasu.”
Ya ce za a gurfanar da Sarkin da aka kama a gaban kotu yau Alhamis 8 ga watan Mayun 2025 domin tabbatar yin adalci da bincike kan lamarin da ya afku.
An zargi Fasto da dirkawa budurwa ciki
A baya, mun ba ku labarin cewa ana zargin wani fasto a cocin 'Christ Apostolic' da ke jihar Ondo da yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 mai nakasa ciki.
'Yan sanda sun damke faston tare da gabatar da shi gaban sarkin garin Oke-Gburowo, inda aka ce ya amsa laifinsa a bainar jama'a.
Iyalan yarinyar da hukumomin tsaro na jihar sun bukaci a tabbatar da cewa an bi hanyar doka domin tabbatar da adalci duba da ƙarancin shekarun yarinyar a cikin al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng