Wani Mutum ya kashe 'yan uwansa 8 da Harsashin Bindiga a 'Kasar Albania

Wani Mutum ya kashe 'yan uwansa 8 da Harsashin Bindiga a 'Kasar Albania

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wani Mutum farat daya ya yi amfani d harsashi na bindiga wajen harbe 'yan uwan sa takwas da ya hadar har da kananan yara biyu kuma ya arce kamar yadda jami'an 'yan sanda na kasar Albania suka bayyana.

Hukumar 'yan sandan a ranar Juma'ar da ta gabata ta bayyana cewa, wannan Matashi Ridvan Zykaj mai shekaru 24, ya harbe 'yan uwansa takwas dake kauyen Resulaj, kimanin kilomita 90 daga kudancin babban birnin Tirana na kasar Albania.

Wani Mutum ya kashe 'yan uwansa 8 da Harsashin Bindiga a 'Kasar Albania
Wani Mutum ya kashe 'yan uwansa 8 da Harsashin Bindiga a 'Kasar Albania

Rahotanni sun bayyana cewa, Ridvan tuni ya dauke sahun sa daga wannan kauye bayan tabargazar da ya aikata da kawowa ba bu masaniyar dalilin aukuwar ta kamar yadda hukumar 'yan sandan ta bayyana.

KARANTA KUMA: Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 5 a jihar Kogi

A halin yanzu hukumar 'yan sandan ta baza hotunan wannan matashi cikin lunguna da sako na kasar domin al'umma su agaza wajen bankado sa daga maboyar sa.Hukumar ta na kuma ci gaba tatsar bayanai wurin iyayen wannan matashi da kuma dangin sa.

Kamar yadda gidan wani talabijin na News24 ya ruwaito, cikin wadanda Ridvan ya salwantar da rayuwar su sun hadar har da wata yarinya 'yan shekara 9, matashiya da kuma Mata 3.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng