Hukumar 'yan sanda ta daƙume wani 'Dan Acaɓa bisa laifin yiwa wata Yarinya 'yar shekara 11 Fyaɗe a jihar Neja
Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Neja, ta daƙume wani ɗan acaɓa, God'stime Okone, bisa laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 11 fyaɗe a wani yanki cikin karamar hukumar Gurara ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan dan kabu-kabu ya yaudari karamar yarinya ne har zuwa shagon sa na kwana, inda ya murkushe ta ta karfi tare da gargadin ta akan zayyanawa wani wannan lamari da ya faru.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari mai cike da takaici ya auku ne a ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata, inda jaridar Northern City ta ruwaito cewa Okone dai ya saba wannan aika-aika shekaru aru-aru kafin dubun sa ta cika.
A yayin amsa laifin sa, Mista Okone ya bayyana cewa sau da dama matasan 'yan mata na tayar ma sa da hankali da har ya gaza rike kwazabar sa da ta jefa sa cikin wannan mummuna lamari.
Yake cewa, "har ya zaman min jiki a duk lokacin da na sanya matasan 'yan mata kyawawa a idanu na, hankali na ya kan yi dubu ya tashi da a halin ya zamto matsala a gare ni da nake gaza hakuri da juriya."
"Wani sa'ilin ma na kan tsaya akan kabu-kabu na mu gaisa da 'yan matan domin samun sa'ida kana na ci gaba da sana'a ta."
Mista Okone dai ya ci gaba da cewa, bai taba kawowa wannan babban laifi ba ne har sai da ya tsinci kan sa a hannun jami'an 'yan sanda, inda a halin yanzu yake da na sani tare da neman yafiyar iyayen wannan yarinya.
KARANTA KUMA: Isa Yuguda da wasu 'yan takara 8 na hankoron maye gurbin kujerar Marigayi Sanata Ali Wakil - INEC
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Muhammadu Abubakar, ya tabbatar da wannan lamari inda Mista Okone ya amsa laifin sa nan take yayin da jami'an hukumar su ka titsiye sa. Za a gurfanar da shi gaban kuliya domin fuskantar hukunci.
A yayin haka kuma, kakakin na 'yan sanda ya shawarci iyayen akan sanya idanun lura tare da tabbatar da masaniyar a duk inda 'ya'yen su Mata suka sanya kafufuwan su domin kare su daga irin wannan miyagun mutane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng