Gwamna Adeleke Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Alkawarin da Tinubu Ya Yi Masa kan Zaben Osun
- Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira shi da kansa lokacin da EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar
- Adeleke ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi masa alkawari kan zaben gwamnan da za a gudanar a jihar Osun
- Gwamnan zai nemi wa’adin mulki na biyu a karkashin jam’iyyar Accord, wadda ke adawa da APC ta Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira shi da kansa yayin da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta rufe asusun gwamnatin jihar.
Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi masa alkawarin gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci.

Source: Twitter
Adeleke ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 11 ga watan Agusta, 2026, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
Gwamnan ya ce ya yaba da kiran da Shugaba Tinubu ya yi masa a lokacin da EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar.
“Na yaba da kiran da Mai Girma Shugaban Ƙasa ya yi a lokacin da EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar. Shugaba Tinubu ya yi mini alkawarin cewa za a gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci."
- Ademola Adeleke.
Adeleke da jam'iyyar Tinubu za su fafata a zabe
Adeleke na neman sake lashe zaben gwamnan jihar Osun a karkashin jam’iyyar Accord, lamarin da ya sanya shi a fafatawa kai tsaye da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta Shugaba Tinubu.
Umarnin EFCC na rufe asusun gwamnatin jihar ya haifar da karin zazzafar siyasa a Osun yayin da ake tunkarar zaben gwamna.
’Yan Najeriya sun mayar da martani
Bayan Adeleke ya bayyana kiran na Tinubu, sakonsa ya jawo martani daga ’yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu suka nuna shakku kan ko shugaban kasa na da ikon tabbatar da irin wannan alkawari ko kuma niyyar yin hakan.
@flourish007 ya ce:
“Gyara kaɗan, Mai Girma Gwamna: ba aikin Shugaban Ƙasa ba ne ya yi ‘alkawarin’ zabe cikin ’yanci da adalci; ba za ka iya yin alkawarin abin da ba ka da iko a kansa ba. Ya kamata ya bar INEC ta gudanar da aikinta ba tare da tsangwama ba, sannan ya umarci ’yan daba da jam’iyyarsa ta dauka su ja da baya. Mun yi watsi da duk wani sakamakon zabe na bogi.”
Shi kuwa @jpobiokafor ya ce:
“Tinubu ya yi maka alkawarin zabe cikin ’yanci da adalci 😂”
@yunghuyt ya kuma tambayi yadda gwamnan zai amince da alkawarin, inda ya rubuta:
“Ta yaya mutumin da bai hau mulki ta hanyar zabe cikin ’yanci da adalci ba zai yi maka alkawarin zabe cikin ’yanci da adalci, kuma ka yarda da shi?”
@Akolawole_8 ya bukaci gwamnan da ya duba matakan tsaro a jihar maimakon dogaro da tabbacin gwamnatin tarayya, yana cewa:
“Jama’a suna son ka, Mai Girma. Abin da suke bukata daga gare ka shi ne tsaronsu. Idan APC ta sayi NPF, ka yi amfani da Amotekun wajen kare kuri’ar jama’a.”
@Akpoyibo16 ya gargadi gwamnan da cewa:
“Ka ci gaba da wasa, zuwa lokacin da ya sake rubuta sakamakon zaben jiharka za ka koya. Tinubu ba ya wasa da kujerarka, yana son kwace ta cikin sauri, ka sani kuma ka samu zaman lafiya.”
A nasa bangaren, @Hassan_xas ya nuna goyon bayansa ga Adeleke gabanin ranar zabe, inda ya ce:
“Za mu yi abin da ya dace ranar Asabar. Ni da iyalina duk za mu kada kuri’a ga Gwamna Ademola Adeleke (Accord) ranar Asabar.”

Source: Twitter
Kwamitin kamfen din Adeleke ya yi zargi
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin yakin neman zaɓen Gwamna Ademola Adeleke ya yi zargin cewa jam’iyyar APC na shirin matsa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) lamba.
Kwamitin ya ce ana shirin matsawa INEC lamba ne domin dakatar da kaɗa ƙuri’a da ƙarfe 12:00 na rana a wasu sassan jihar Osun.
Asali: Legit.ng