Harin Saudiyya ya salwantar da rayukan 'Kananan Yara 40 a 'Kasar Yemen

Harin Saudiyya ya salwantar da rayukan 'Kananan Yara 40 a 'Kasar Yemen

Cikin kwaranyar hawaye ta dubunnan mutane, anyi jana'izar yara kimanin 40 da ajali ya katse masu hanzari yayin da mayakan kasar Saudiya suka kai wani mummunan hari kan wata mota dauke da al'umma a Arewacin Kasar Yemen.

Aukuwar wannan mummunan hari a birnin Saada da ta salwantar da rayukan mutane 51 a ranar Alhamis din da ta gabata, ta kuma raunata kimanin yara 46 cikin mutane 79 da suka jikkata kmaar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta duniya ta bayyana watau Red Cross.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta ABC ta bayyana, aukuwar wannan hari tayi mafificin muni kan gamagarin mutane yayin da kasar Saudiya da Mayakan kungiyar Houthi ke ci gaba da fafatawa tun shekaru uku da suka gabata.

Yayin haƙa kaburburan wadanda ajali ya katsewa hanzari a 'Kasar Yemen

Yayin haƙa kaburburan wadanda ajali ya katsewa hanzari a 'Kasar Yemen

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da kuma majalisar dinkin duniya na ci gaba da bayyana fushi gami da ƙyama kan aukuwar wannan mummunan hari cikin wata kasuwa a garin Dahyan da Mayakan Houthi suka kafa daular su.

Sai dai daga babban birnin Riyadh na kasar Saudi rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da wannan hari ne bisa tsari na daidai sakamakon manufa ta tarwatsa shugabannin kungiyar Houthi dake birnin na Saada.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya kashe 'yan uwansa 8 da Harsashin Bindiga a 'Kasar Albania

Kididdigar Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, a halin yanzu wannan rikici ya salwantar da rayukan kimanin mutane 10, 000 wanda mafi akasarin su fararen hula na da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Amurka da gwamnatin wasu kasashen nahiyyar Turai sun bayyana kunyar sa karara dangane da munin wannan hari sakamakon ruwa da tsaki da suke da shi na tanadar makaman yaki ga kasar ta Saudiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel