Wata Mahaifiya ta manta jaririn dan watanni 3 cikin Mota, sai gawar sa ta tsinta
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, wani jariri dan watanni 3 da haihuwa ya riga mu gidan gaskiya cikin wata Mota yayin da Mahaifiyar sa ta manta da shi wajen kuskuren ajiye sa a gidan raino.
Mahaifiyar wannan jariri Aiden Miller, ta fahimci babban kuskuren ta ne bayan ta tashi daga wurin aiki ta a wani kanti, inda tayi kacibus da jaririn ta a bayan Motar ta da har ya fara samami kamar yadda mai gidan ta Aaron Miller ya bayyana.
A halin yanzu dai hukumar 'yan sanda tuni ta fantsama cikin binciken wannan lamari mai kunshe da mamaki gami da tausayi.
An tabbatar da mutuwar wannan jariri ne a wani Asibiti dake yankin Arewacin Louisville a garin Kentucky na kasar Amurka.
KARANTA KUMA: Abin da sauyin shekar Kwankwaso ke nufi ga jam'iyyar APC a jihar Kano - Ganduje
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan Mata tana da 'ya'ya biyu ne da ta saba ajiye su a gidajen raino daban-daban, inda bayan ajiye 'yar ta ta farko ta sha'afa wajen ajiye jaririn na ta da ya sanya ta manta da shi cikin motar ta.
Mahaifiyar cikin razani ta yi kacibus da gawar dan na ta ne a kujerar baya bayan da ya shafe sa'o'i masu tsawo cikin motar da ta yi ajiyar ta karkashin rana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng