Wata Babbar Mota ta muƙurƙushe Motoci 15 a Babbar Hanyar garin Keffi zuwa Abuja
Mun samu rahoton cewa, matafiya dake bibiyar babbar hanyar Abuja zuwa garin Keffi sun tagayyara a daren ranar Litinin din da ta gabata sakamakon aukuwar wani mummunan hatsari ya hadar da kimanin motoci 15 daban-daban.
Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito sun bayyana cewa, wannan hatsari ya auku ne a sanadiyar kwacewar kan wata babbar motar daukan kaya da ta muƙurƙushe motoci 15 a kan babbar hanyar ta garin dake garin Abuja.
Wannan hatsari ya auku ne da misalin karfe 9.00 na daren ranar Litinin din da ta gabata da yayi sanadiyar kawo tsaiko na jerin gwanon motoci wanda sai da jami'an hukumar kula da lafiyar hanyoyi ta FRSC suka kai ruwa rana wajen bude hanyar ga matafiya.
KARANTA KUMA: An samu naƙasun Wutar Lantarki a Najeriya - Fashola
Shugaban hukumar ta FRSC, Mista Bisi Kazeem, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari sai dai bai bayar da tabbacin asarar da hatsarin ya janyo ba yayin hada wannan rahoto.
Ya kuma shawarci matafiya masu sha'awar bi ta wannan hanya akan su yi shataletalen bin gadar garin Karu domin gujewa tsaiko a yayin tafiyar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng