Abubuwa Sun Kara Birkicewa Trump, Kamfaninsa Ya Tafka Babbar Asara
- Kamfanin TMTG na Donald Trump ya samu kudin shiga $1.7m tsakanin Afirilu da Yuni 2026, amma ya yi asarar $238m
- Asarar kamfanin ta karu zuwa $644m a watanni shidan farko na 2026, yayin da Truth Social ke ci gaba da samun masu amfani kadan
- Kamfanin na shugaban kasar Amurka ya ce $190.4m na asarar sun samo ne daga kadarorin dijital da hannayen jari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Kamfanin yada labarai na Shugaban Amurka Donald Trump, Trump Media & Technology Group (TMTG), ya bayyana cewa ya yi asara.
Kamfanin na Trump ya bayyana cewa ya yi asarar dala miliyan $238 a zangon watanni uku na biyu na 2026, duk da samun kudin shiga na $1.7m.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce hakan na kunshe ne a cikin rahoton da ya shigar wa Hukumar Kula da Kasuwannin Hannayen Jari ta Amurka (SEC) ranar Litinin, 10 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: INEC ta yi wa jam'iyyu adalci kan mika sunayen 'yan takarar gwamna da majalisa
TMTG ya yi babbar asara
TMTG ya ce mafi yawan asarar ta samo ne daga dala miliyan 190.4 da suka shafi asarar da ba a tabbatar da ita ba kan kadarorin dijital, kadarorin dijital da aka jinginar da su da kuma hannayen jari.
Kamfanin ya kuma yi asarar dala miliyan 11.7 ta hanyar abin da ya kira “accreted interest”, wato kudin ruwa da ba a biya ba wanda ake kara wa babban bashin, yayin da karin dala miliyan 8.1 ya shafi biyan diyya ta hannun jari.
TMTG ya ce kudin shigar da ya samu tsakanin Afirilu da Yuni ya karu da 89% idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, amma asarar ta ci gaba da zarce kudaden da kamfanin ke samu.
Daga ina kudin shiga suka fito
A cewar bayanan da aka shigar wa SEC, kusan dukkan kudin shigar TMTG sun fito ne daga bangaren kafafen yada labarai.
Kamfanin ya samu dala miliyan 1.43 daga tallace-tallace, yayin da kudin rajista ya kai $179,500.
Sababbin alkaluman sun sa jimillar asarar TMTG a rabin farko na 2026 ta kai dala miliyan 644, yayin da kudin shigar kamfanin ya tsaya kan dala miliyan 2.5.
Hannayen jarin TMTG, wadanda ake sayar da su a NASDAQ karkashin alamar “DJT”, sun fadi da 8% a lokacin rufe kasuwar ranar Litinin.
Abubuwan da TMTG ke gudanarwa
TMTG na da kafar sada zumunta ta Truth Social, da manhajar kallon bidiyo ta Truth+, da kuma kamfanin harkokin fasahar hada-hadar kudi Truth.Fi.
A cikin shekarar da ta gabata, kamfanin ya fadada harkokinsa zuwa wasu fannoni, ciki har da kudin intanet, sannan daga ranar 1 ga Agusta ya shiga harkar bayanan kasuwa ta hanyar wata sabuwar manhajar biyan kudin rajista mai suna Truth API.
Truth API na bai wa masu zuba jari damar samun sakonnin da ake wallafawa a Truth Social cikin sauri, inda Trump ke yawan wallafa bayanai kan manufofin gwamnati da za su iya shafar kasuwanni, ciki har da harajin shigo da kaya da kuma yakin Amurka da Isra'ila da Iran.

Source: Getty Images
Trump ya mika bukatarsa ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya mika sabuwar bukatarsa ga kasar Iran.
Shugaban kasar na Amurka, Donald Trump, ya bukaci Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta biya diyya kan mutanen da ya ce kasar ta kashe
Asali: Legit.ng

