Amai da Gudawa Ya Bulla Tsakanin Sojojin Isra'ila Mata, Dakaru 30 Sun Tsure

Amai da Gudawa Ya Bulla Tsakanin Sojojin Isra'ila Mata, Dakaru 30 Sun Tsure

  • Kimanin sojojin mata 30 sun kamu da amai, gudawa da ciwon ciki a wani sansanin sojin Isra’ila da ke kudancin ƙasar
  • An dakatar da atisayen sojoji na ɗan lokaci bayan yawan masu fama da alamomin rashin lafiya ya ƙaru a sansanin Sde Boker Gadna
  • Wata sojar sama ta zargi rashin tsaftar wuraren dafa abinci da yawan kwari da kyankyasai da haddasa matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kudancin Isra’ila – Kimanin sojojin mata 30 da suka haɗa da kwamandoji da sabbin sojoji sun kamu da rashin lafiya a sansanin Sde Boker Gadna da ke Kudancin Isra’ila.

Sojojin sun nuna alamomin amai, gudawa da ciwon ciki, lamarin da ya sa aka dakatar da wasu ayyukan atisaye a sansanin.

Wasu sojojin Isra'ila a bakin aiki
Sojojin Isra'ila a lokacin wani aiki a shekarun baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An dakatar da atisaye a sansanin

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sojoji sun yi gumurzu da 'yan ta'adda a daji, sun ceto mutane

Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran JFeed sun ce jami'ai sun dakatar da atisayen ranar Litinin bayan yawan sojojin da suka kamu da rashin lafiya.

Sojojin da suka kamu da alamomin rashin lafiyar sun samu kulawar likitoci a sansanin. An kuma sanya kammala binciken lafiyar sojojin a matsayin sharadin komawa ayyukan atisaye.

An kai wasu sojoji asibiti

An ce wata motar bas ta ɗauki wasu daga cikin sojojin da ke fama da irin waɗannan alamomi zuwa wani asibiti ko cibiyar lafiya da ke yankin.

Sansanin Sde Boker Gadna na karɓar matasa da ke shirin shiga aikin soja ta shirin Gadna. Shirin na ɗaukar kusan mako guda, inda ake koyar da matasa wasu abubuwan da suka shafi rayuwar soja.

Benjamin Netanyahu a Isra'ila
Benjamin Netanyahu da wasu jami'an Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sansanin ya kuma karɓi wasu masu koyon aikin soji da aka saba gudanar da kwas ɗinsu a sansanin rundunar sojin sama ta Isra’ila da ke Ovda.

Roya News ta wallafa cewa wata sojar sama da ta shafe makonni a sansanin ta yi korafi kan yanayin wuraren da ake dafa abinci.

Ta ce:

"Wuraren dafa abincin nan suna da datti kuma cike suke da kwari da kyankyasai, kuma dama lokaci ne kawai ya rage kafin irin wannan abu ya faru."

Kara karanta wannan

An kama dan bindiga makare da Naira da dalolin Amurka yana shirin guduwa

Martanin rundunar sojin Isra'ila

Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa wasu sojoji a sansanin sun nemi kulawar likita bayan sun fara jin rashin lafiya.

Ta ce duk sojan da ya nuna alamomin rashin lafiya ya samu kulawar farko a sansanin. Rundunar ta kuma musanta ikirarin cewa an hana wasu sojoji shiga ɗakin cin abinci.

Ta ce ana ba dukkan sojojin abinci gwargwadon yanayin lafiyarsu, yayin da waɗanda suka nuna alamomin rashin lafiya ke samun kulawar da ta dace da bukatunsu.

Trump na son Iran ta biya diyya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai nemi Iran ta biya diyya kan mutuwar dubban sojojin Amurka da fararen hular Iran da aka kashe cikin shekarun baya.

Trump ya ce buƙatar biyan diyya na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake buɗe Mashigin Hormuz.

Ya kuma nemi a biya diyya bayan masu shiga tattaunawar Iran sun gabatar da irin wannan buƙata kan barnar da yaƙin watanni biyar ya haddasa wa ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng