Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo

Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa hukumar 'yan sanda ta jihar Enugu, ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani matashi dan shekaru 24 da ya kashe kansa bayan ya sha tabar wiwi ta yi ma sa karo.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Ebere Amaraizu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Enugu a ranar Asabar din da ta gabata.

Wannan lamari ya auku ne a kauyen Ameke dake yankin Enu-Oduma na karamar hukumar Aninri ta jihar a ranar 22 ga watan Agusta kamar yadda kakakin 'yan sandan ya bayyana.

Mista Amaraizu ya bayyana cewa, wannan matashi, Ebube Chukwu, ya salwantar da rayuwar sa ne bayan ya sha tabar wiwi da ta shahara da sunan 'Igbo' kamar yadda ya saba a koda yaushe.

Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo
Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo

Rahotanni sun bayyana cewa, Marigayi Chukwu ya salwantar da rayuwar sa ne ta hanyar rataye kansa jikin wata bishiya cikin dokar daji na Obokola dake tsakanin garuruwan Amorji da kuma Ameke Oduma.

KARANTA KUMA: Mambobi 5000 na jam'iyyar PDP sun sauye sheƙa zuwa APC a jihar Legas

Sai dai bincike ya tabbatar da cewa, ana zargin yawaitar shaye-shayen tabar wiwi ta marigayi Chukwu da ya saba ce ta yi sanadiyar salwantar rayuwar sa.

A halin yanzu hukumar 'yan sanda ta ci gaba da tsananta bincike domin tabbatar da gaskiya ta sanadiyar mutuwar wannan matashi kamar yadda Mista Amaraizu ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel