Wani Mahaukaci ya Kashe 'Dan tsubbu a jihar Anambra

Wani Mahaukaci ya Kashe 'Dan tsubbu a jihar Anambra

Rahoto ya zo mana cewa an yi dimuwa gami da tashin hankali yayin da wani Matashi mai karancin hankali ya sheke wani Malamin tsubbu murus har lahira a garin Oba Aguleri dake karamar hukumar Anambra ta Gabas.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana wannan mummuna laifi na kisan gilla ya yi sanadiyar zanga-zanga da ta salwantar da dukiya mai tarin yawa gami da kawo tsaiko na hada-hadar kasuwanci a yankin jihar.

Lamarin dai ya auku ne yayin da wannan malamin tsubbu da aka sakaya sunan ya turke wata akuya da ya nufaci sadaukar da jinin ta wajen aiwatar da sihiri kuma ya kama gaban sa zuwa kasuwa domin cefanen saurar ababe da yake bukata.

A yayin dawowar sa ne ya nemi wannan dabba ya rasa inda aka labarta ma sa cewa ai wani taɓaɓɓe ya yi awon gaba da ita. Nan da nan ya bi sahun sa har gida domin bibiyar dalilin wannan lamari mai ban takaici.

Wani Mahaukaci ya Kashe 'Dan tsubbu a jihar Anambra
Wani Mahaukaci ya Kashe 'Dan tsubbu a jihar Anambra

Ba tare da aune ba Malamin na tsaka da titsiye Matashin kan dalilin da ya sanya ya kwance ma sa akuyar sa, sai kawai makami na adda ya hanga da ta sanya ya nemi tsira da kafafun sa da bai yi wani dogon taku ba sai saukar sara ta ko ina yaji a jikin sa.

Rahotanni sun bayyana cewa, nan take Malamin tsubbu ya ce ga garin ku nan da lamarin ya fusata Matasan yankin yayin da suka nemi daukar fansa da sai jami'an tsaro ne suka yi gaggawar shiga cikin lamarin.

KARANTA KUMA: Jihar Gombe na fitar da Macizai 400 zuwa 'Kasar Ingila a kowane Wata

Legit.ng ta fahimci cewa, ruwa da tsakin jami'an tsaro ne ya kwantar da wannan tarzoma wadda da sai dai wani labarin na daban ba wannan ba.

Kakakin 'yan sandan jihar, Haruna Muhammad, ya tabbatar da wannan lamari inda ya bayyana cewa, tuni wannan Matashi ya shiga hannu tare da wasu mutane uku da suka yi yunkurin daukar doka hannun su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel