Zaben 2027: Obi, Kwankwaso Sun Zauna da Yan Takarar Gwamna 25 a NDC
- 'Yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa, Peter Obi da Rabi’u Kwankwaso sun gana da wasu daga cikin ’yan takarar gwamnan NDC
- An gano abin da manyan jam'iyyar suka tattauna yayin da ake shirin tunkarar babban zaben 2027 wanda za a fara kamfen a cikin 'yan makonni
- Shugabannin NDC sun bukaci hadin gwiwa tsakanin yakin neman shugaban kasa da na gwamnatocin jihohi a kokarin da suke yi ya kayar da APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, tare da abokin takararsa, Rabi’u Kwankwaso, sun gana da manyan ‘yan jam’iyyar gabanin fara yakin neman zaben 2027 a hukumance.
An gudanar da taron ne da daren Litinin a Abuja 10 ga watan Agusta, 2026, inda aka tattauna kan dabarun karfafa tsarin yakin neman zaben jam’iyyar a matakin kasa da jihohi.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, inda ta ce taron ya mayar da hankali ne kan shirye-shiryen dabarun yakin neman zabe da kuma tantance irin shirin da jam’iyyar ta yi gabanin kakar zaben mai zuwa.
Yan takarar NDC sun zauna a Abuja
Rahoton da Daily Post ta kawo ya ce NDC ta jaddada muhimmancin gudanar da yakin neman zabe da murya daya inda ta ce akwai bukatar a samu kyakkyawar alaka tsakanin yakin neman kujerar shugaban kasa da na ’yan takarar gwamnonin jihohi.

Source: Facebook
A cewar jam’iyyar, hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa dukkanin matakan takarar jam’iyyar suna tafiya ne bisa tsari guda domin kara mata damar samun nasara a zaben 2027.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai wani jigo a jam’iyyar, Buba Galadima, da shugabannin NDC na jihohin Kebbi da Sokoto, Alhaji Mustapha Umar da Alhaji Bello Sani Yabo.
Yan takarar gwamnoni a NDC sun hallara
Haka kuma, sama da ’yan takarar gwamnan jihohi 25 na jam’iyyar sun halarci taron da aka gudanar a Abuja domin karfafa tafiyarsu gabanin fara kamfen.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyu ke kara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027, yayin da ake sa ran yakin neman zabe zai kara daukar zafi a fadin kasar.
Shugabannin NDC sun nuna cewa hadin kan dukkannin ’yan takarar jam’iyyar da masu ruwa da tsaki zai kasance muhimmin bangare na kokarinsu na samun nasara a zabukan da ke tafe.
'Yan NDC sun yi watsi da sulhu
A wani labarin, kun ji cewa wasu fusatattun mambobin NDC daga jihar Edo sun fito fili sun ki aminta da kwamitin sulhun da jam'iyyar ta kafa masu yayin da ake shirin zaben 2027 mai cike da adawa.
Mambobin sun bayyana cewa kafa kwamitin yunkuri ne kawai na tilasta masu karbar sakamakon zaben fitar da gwani wanda suke ganin ba a yi masu dai-dai ba, sannan ba su da niyyar amincewa da shi.
‘Yan jam’iyyar jaddada cewa ba za a samu zaman lafiya ko hadin kai na gaskiya a kwamitin Pat Utomi da Buba Galadima wanda aka kafa domin tabbatar da an yi sulhu tare da warware matsalolin takara.
Asali: Legit.ng

