Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuka 5 a jihar Kogi
Kimanin rayukan mutane biyan ne suka salwanta yayin aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kauyen Ogbabo dake kan babbar hanyar Ajaokuta a jihar Kogi.
Mista Olusegun Martins, shugaban hukumar kula da tsaron manyan hanyoyi, shine ya tabbatar da wannan lamari yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya, inda ya ce akwai kimanin mutane biyu da suka jikkata a hatsarin.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hatsari ya auku ne da misalin karfe 3.30 na yammacin ranar Juma'ar da ta gabata wanda ya hadar da wasu motoci biyu kirar Toyota Sienna mai lambar EPE 307 XU da kuma wata motar mai lambar AK ILIKA 1 tare da tambarin NAOWA (Nigerian Army Officers Wives Association).
Mista Martins ya ci gaba da cewa, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kurkusa inda suke karbar magani yayin da aka killace gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a ma'ajiyar gawa ta asibitin.
KARANTA KUMA: Da tsarin Doka ta Dimokuradiyya za a tsige Saraki - Oshiomhole
Legit.ng ta fahimci cewa, tuni hukumar ta fara gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin wannan mummunan hatsari.
Sai dai wani mashaidin wannan lamari da ya bukaci a sakaya sunan sa ya shaidawa manema labarai cewa, hatsarin ya auku ne a sakamakon kaucewa ramuka daga bangaren direbobin motocin biyu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng