Gwamnan APC Ya Kaƙaba Harajin N150m kan Bola Tinubu da Wasu Yan Takara a Zaben 2027

Gwamnan APC Ya Kaƙaba Harajin N150m kan Bola Tinubu da Wasu Yan Takara a Zaben 2027

  • Gwamnatin jihar Kogi ta amince da N150m a matsayin kuɗin yada fastoci da sauran abubuwan talla na yan takarar shugaban kasa a 2027
  • ’Yan takarar Sanata za su biya N50m, ’yan majalisar wakilai N30m, yayin da ’yan majalisar jiha za su biya N5m
  • Gwamnati ta ce za a cire tallan siyasar da aka sanya ba tare da izini ba tare da hukunta masu karya doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kogi karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Ododo ta kayyade harajin da kowane dan zai biya domin samun izinin kamfe ta hanyar yafa fastoci da sauran abubuwan talla a fadin jihar.

Gwamnatin ta amince da Naira miliyan 150 a matsayin kudin sanya allunan talla da sauran tallace-tallacen yakin neman zaben ’yan takarar shugaban kasa a jihar gabanin 2027.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Obi, Kwankwaso sun zauna da yan takarar gwamna 25 a NDC

Ododo.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo a fadar gwamnati Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Source: Twitter

Leadership ta ce kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana hakan a Lokoja bayan wani taron masu ruwa da tsaki da masu gudanar da harkokin tallace-tallacen siyasa a jihar

Sabon tsarin kudaden ya tanadi cewa ’yan takarar Sanata za su biya Naira miliyan 50, yayin da ’yan takarar Majalisar Wakilai za su biya Naira miliyan 30.

’Yan takarar Majalisar Dokokin Jiha kuma za su biya Naira miliyan 5 domin sanya allunan talla, fastoci, riguna, huluna da sauran kayan yakin neman zabe.

Kudin zabukan kananan hukumomi

Gwamnatin jihar ta kuma ce sabon tsarin ya shafi zaben kananan hukumomin da za a gudanar a watan Oktoban 2026, cewar rahoton PM News.

A karkashin tsarin, ’yan takarar shugabannin kananan hukumomi za su biya Naira miliyan 2, yayin da ’yan takarar kansiloli za su biya N300,000 domin tallan yakin neman zabensu.

Fanwo ya ce an bullo da kudaden ne domin daidaita harkokin tallan siyasa, tabbatar da bin dokokin sanya allunan talla da kuma kara wa gwamnatin jihar kudaden shiga.

Kara karanta wannan

Soke kudin tsaro da wasu sauye sauye da ADC za ta kawo idan ta ci zaɓen 2027

Ya bayyana cewa an yi la’akari da kudaden da ake karba a wasu jihohi kafin amincewa da sabon tsarin, yana mai cewa kudaden sun dace da girman yakin neman zaben da kuma yawan mutanen da tallan zai iya isa gare su.

APC ba za ta samu rangwame ba

Kwamishinan ya gargadi jam’iyyun siyasa da ’yan takara cewa duk wanda ya sanya allunan talla ko fastocin yakin neman zabe ba tare da biyan kudin da aka kayyade da kuma samun izinin da ya dace ba, zai fuskanci hukunci.

APC .
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin jihar Kogi da Najeriya Hoto: @OfficialAPCNIG
Source: Twitter

Ya jaddada cewa dokar ta shafi dukkan jam’iyyun siyasa, ciki har da jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

kai dan takarar APC ne kuma ba ka biya kudin da aka kayyade ba kafin sanya allunan tallanka ko fastoci, za mu cire su kuma za a gurfanar da kai,” in ji Fanwo.

Gwammatin Kogi ta rufe kasuwanni

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi ta sanar da rufe wasu zaɓaɓɓun kasuwanni da tashoshin mota a sassan Kogi ta Yamma.

Wannan mataki wanda na ɗan lokaci ne, an ɗauke shi ne domin gudanar da gagarumin aikin tsaro na fatattakar ƴan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262