Hukumar 'Yan sanda ta damuƙe Masu neman Maza 6 a jihar Abia

Hukumar 'Yan sanda ta damuƙe Masu neman Maza 6 a jihar Abia

Mun samu cewa hukumar 'yan sanda ta cikwikwiye wasu mutane 6 masu neman maza cikin Otel din City Gobal da misalin karfe 2.00 na daren ranar Alhamis din da ta gabata a jihar Abia.

Mista Anthony Ogbizi, kwamishinan 'yan sanda na jihar shine ya bayyana hakan yayin gabatar da wannan miyagun mutane ga manema labarai na jaridar The Punch a garin Aba.

Wannan miyagun mutane sun hadar da; Fred Ndubuisi, Anyanwu Chidera, Kamsiriochukwu Onuoha, Anderson Emeruwa, Sampson Nwadike da kuma Nnadi Promise kamar yadda Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana.

Hukumar 'Yan sanda ta damuƙe Masu neman Maza 6 a jihar Abia
Hukumar 'Yan sanda ta damuƙe Masu neman Maza 6 a jihar Abia

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sandan ta samu nasarar cafke wannan Matasa yayin da Mamallakin Otel din ya yi korafin gaggawa yayin da suke tsaka da sumbutar junan su a bainar jama'a.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta biya Maƙudan Kuɗi na Fansar 'Yan Matan Dapchi

A yayin tsananta bincike hukumar 'yan sandan ta gano cewa wannan Matasa 'yan wata kungiya ce da suka saba haurowa jihar Abia da makotan jihohi inda da suke aikata wannan mummuna alfasha.

Kwamishinan 'yan sandan ya kuma nemi ma'aikatan wannan Otel akan su gabatar da gamsashiyar shaida akan wannan miyagu inda za a gurfanar da su gaban kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel