Babban Ma'aikacin 'Karamar hukuma ya kashe kansa murus a jihar Ekiti

Babban Ma'aikacin 'Karamar hukuma ya kashe kansa murus a jihar Ekiti

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, mun samu rahoton cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne wani babban ma'aikacin karamar hukuma, Michael Kayode Bamisaye, ya sheke kansa murus har lahira a gidan sa dake birnin Ado-Ekiti na jihar Ekiti.

Mun samu cewa, Bamisaye wanda shine shugaba mai kula da harkokin kudi na karamar hukumar Ise/Orun, ya kashe kansa ne ta hanyar tsunduma kansa cikin wata rijiya dake gidan sa daura da makaratar Tinuola Maximun dake kan babbar hanyar Afao a birnin na Ado-Ekiti.

Rahotanni sun bayyana cewa, Marigayi Bamisaye sai ya da ya kwankwadi ruwan Siminti yayin yunkurin kashe kansa, wanda daga bisani ya nemi cimma wannan mummunan buri na sa har cikin rijiya.

Babban Ma'aikacin 'Karamar hukuma ya kashe kansa murus a jihar Ekiti
Babban Ma'aikacin 'Karamar hukuma ya kashe kansa murus a jihar Ekiti

Legit.ng ta fahimci cewa, an samu tsaikon gudanar da aikace-aikace a shelkwatar karamar hukumar ta Ise/Orun, yayin samun rahoton wannan mummunan rashi da kawowa yanzu babu tabbataccen dalilin aukuwar sa.

KARANTA KUMA: Rayuka 42 sun salwanta a wani sabon hari cikin jihar Zamfara

Bamisaye dai shine ma'aikacin gwamnatin na uku da ya riga mu gidan gaskiya a karamar hukumar Ise/Orun cikin wannan shekara, inda ragowar biyun suka ce ga garin ku nan ta makamanciyar wannan mummunar hanya.

Sai dai manema labarai ba su samu damar ganawa da kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Caleb Ikechukwu, domin tabbatar da wannan lamari ba sakamakon neman sa ta hanyar wayar tarho da bai tabbata ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng