Wani Mahaifi dan shekara 45 ya yiwa 'Diyar sa ciki a Garin Sagamu

Wani Mahaifi dan shekara 45 ya yiwa 'Diyar sa ciki a Garin Sagamu

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta jihar Ogun, ta cafke wani Mahaifi dan shekara 45 da yake zaman daduro da diyar sa da lamarin mai cike da takaici har ya kai ga dankara ma ta juna biyu.

Hukumar 'yan sandan ta reshen garin Sagamu ta cafke Julius Ochim ne bisa laifin keta haddin diyar sa da ya saba tun tana 'yar shekara 9 a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan rashin sanin mutuncin kai da abin kunya ya fara aukuwa ne tun a shekarar 2009 yayin da Mahaifiyar wannan Yarinya ta riga mu gidan gaskiya.

Wani Mahaifi dan shekara 45 ya yiwa 'Diyar sa ciki a Garin Sagamu
Wani Mahaifi dan shekara 45 ya yiwa 'Diyar sa ciki a Garin Sagamu

Lamarin dai ya ci gaba da aukuwa ne a yayin da wannan Mahaifi ya rika yiwa diyar ta sa yaudara ta barazanar sabubba na al'adun su da ka iya shafar ta muddin ta ki amincewa da bukatar sa.

A yayin da wannan Mahaifi ya shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda, ya amsa laifinsa tare da cewar sharrin Shaidan ya jefa sa cikin wannan aika-aika.

KARANTA KUMA: Za mu sayar da dukkanin kadarorin da muka ƙwato hannun 'Yan harambe - Buhari

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa, Mahaifin wannan yarinya ya amsa cewar ba ya da nufin aurar da ita ga kowa domin ci gaba da amfani da ita.

Kazalika Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahmed Iliyasu, ya bayar da umarnin mika Mista Julius hannun hukumar kula da harkokin keta haddin yara ta jihar domin ci gaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng