Uba da 'Da sun yi taron dangin keta haddin wata Budurwa 'Yar shekara 13 a jihar Benuwe
Za ku ji cewa wani babban lakcara na Kwalejin Ilimi ta garin Ugbokola, Andrewa Ogbuja dan shekara 51, ya gurfana gaban kuliya bisa aikata mummunan laifi na keta haddin wata budurwa da ke masa hidimar aikace-aikacen gida.
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai sa hannun wani Matashin ɗa ga Mista Andrew, wanda shima ya bayar da tasa gudunmuwar wajen cin zarafin wannnan Budurwa da tuni ya arce abin sa.
Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya bayyana, an gurfanar da Mista Andrew ne gaban wata Kotun Majistire dake Birnin Makurdi a ranar Juma'ar da ta gabata bayan da 'yan wannan Budurwa suka shigar da korafin su.
Sai dai Mista Andrewa ya nemi alkalin Kotun, Mista Sam Kwen, kan yi masa sassauci wajen zartar da hukuncin tare rokon bayar da belin sa domin su sulhunta wannan lamari a tsakanin sa da ma su korafi.
KARANTA KUMA: Obasanjo na daya daga cikin kalubalen da muke fuskanta a Najeriya - Tinubu
A yayin da lauyan wanda ake tuhuma, David Ojile, ke ci gaba da mika kokon barar sa a kotun, alkalin kotun ya bayar da umarnin ci gaba da tsare da Mista Andrewa a gidan kaso dake birnin Makurdi tare daga sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Satumba.
A yayi haka kuma Legit.ng ta fahimci cewa, jami'ar birnin Minna dake jihar Neja, ta fatattaki wani Lakcara, Omananyi Yunusa, bisa sanya hannun sa dumu-dumu wajen keta haddin wata dalibar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: hhttps://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng